Kwanakin baya muka hadu a Kaduna don murnar cikar farfesa Ibrahim malumfashi shekaru a duniya.kafin nan na bi wani rubutun da ya rika yi, na cikarsa wadan nan shekaru a filinsa da ke jaridar AMINIYA.rubutun ya burge ni yadda ya tuna baya. Wannan yasa na tuno da wani rubutun tuna baya. Dana buga a mujallar Matasa.wadda ta fito a shekarar 2009.Na ga yakama ta in sake buga shi ba canji a filin HANTSI don makaranta na su dan dara.
Musammam wancan da aka buga sai da dan kincimi ya neme ni y ace ai na rage labarin a wani waje a labarin don kuwa ai said a na…………….. NI kuma nace ai wannan sirri ne. a sha karatu lafia amma don Allah kar kai man dariya.
Kakannimu da muka tashi a wajensu sun horas damu zumunci,wanda mukan je gaida dangi kowa ce jumma a.kullum aka gama salla zamu rako kakanmu gida tare da sauran jama a.daga nan zamu ci abinci rana ,sannan sai mu shiga gari gaida yan uwa da abokan arziki.
An saba da sanin gaida dangi da yaran da aka ba tarbiya irin wannan kanzo don haka zaka ga dangi kana aje kudi wadanda akan raba ma yan ziyarar jumma a.wasu kuma kana je kayan malaki ne wanda suke ba yaran ,yan uwa kanyi amfani da wannan dama su gargradi yada su kara kara kokari a wajen karatunsu.su kan kuma amfani da ziyarar wajen yi masu nasihohi akan rayuwa da nasararta.
Da yake dangin nawa yawa garesu,ni da wasu abokaina su muntari na kan barya muka raba ziyarar dangin namu zuwa gida biyu,yau in munje wani sashen wani lokaci kuma sai muje wani barayin,
Mukan farad a unguwar sagi, wadda ke cikin birni wanda yanzu a akai kasuwar cake a kusa da anguwar.sai mu fada bakin gida sai kuma mu shigo ta marnar kadabo mu rankaya zuwa marnar tafki,mu bi ta filin bugu mu ratsa chake mu isa sararin tsako. Mushogo longuna mu je kasuwa muna takawa dai daya domin akwai tsaba aljifunan mu.muna iya sayen duk wani kayan dadi d muke sha a wa.wani satin kuma sai mu bi ta wani layin.
Wata juma a bayan mun raka mallam gida[kakanmu]na nemi mai kan tabarya[bad nickname na muntari]
Ban ganshi ba.sai kawai na fito yawo na ni daya, wannan satin zanbi ta kofar soro ne in bi layin unguwannin dake wannan zagayen ,na taho har bakin kofar soro a filin na kofar soro sai na gawani mai wasa da maciji,na ko tsaya kallo,yayi ta abubuwan jan hankali kuma masu ban mamaki daga can sai ya koma tallar magani,yana tallar wani magani wais hi”” ki bugu,””wata lay ace zaka saya zaka je a dinke maka ita,mai maganin yace in kana tare da layar kowa yazo bugunka hannunshi zai sage har sai kayi masa mari goma ko kuma ya lashi takashinka.
Nan da nan sai naji ina da bukatar sayen wannan laya,ba kudi aljifuna ai sai na ruga gidajen zumunci da zanyi na shiga ta kofar soro na fado saulawa na biyo tab akin asibiti na zo galadunci .na dawo wurin mai saida maganin “”ki bugu””duk inda gidan dangin da aka nemi a tsaida ni hira ko kuma wata nasiha sai ince sauri nake ayi man hakuri sai wani sati in na dawo,
Na iske mai magani ya tashi yana ta saurin hada kayansa na mika masa kudi na amshi laya daya yayi mani bayanin daki yadda zanyi da ita.na karba na kama hanyar gida ina ji na da wani sabon karfi.dama inajin kamar duk an raina ni saboda duk cikin abokaina nine dan karami acikinsu.’’zan nuna masu ni kodagone a ganka a raina ataka ka karya mutun’’ina fadi azuciya ta,
Ina kuma tafiya ina tsara ya zangwada wannan karfin iko nawa yadda kowa zai sani kuma a shiga taitayi?in saka wannan in kwance in tsara wancan in warware,abokaina kowa na dauko sai inga ba wani dalilin fada dashi.
A gabashin unguwarmu akwai wani tafki da ake kira lahirar makafi saboda raminsa da kuma girmansa,a kusa da wurin akwai wani mai saida dafaffun kanu, a gidan wasu yan damben gargajiya na sauka,a cikin yan damben akwai wani da ake kira Iro dan kincimi.
Shi iro dankincimi kowa ya sanshi a yankin saboda yana yawan kashe mutane a dambe.amma a mu amala ba ruwanshi da kowa mutumin kirki ne,a siffa kuwa abin tsoro ne, domin kuwa gashi gajere.dirarre.kuma kakkarfa,kuma baki ne wulik. Mutumin wani gari mai suna doso a jamhuriyar nijar.
Zuciya ta sai kawai nayi shawarar cewa in har nayi fada da dan kincimi a gaban jama a lallai zan kira lamba.don haka sai kawai naje na tsokani dan kincimi cikin tsokanar hard a dangwalar masa hanci har kuwa na fusata shi,har y ace in fadi ina nakejin zamu iya haduwa a kara?na wani Harare shin a ce mu hadu dandalin wasanni dake wajen gidan waya bayan anyi isha I,
A yankin baki daya nan yara tsarrakinmu ke haduwa suyi wasa . akwai wani katon fili.zakaga yara gungu gungu suna wasanni kala kala,irinsu tahole da bida da was an burum akanyi kuma wasa mai suna ya zagi Ahmad,was an shi ya zagi Ahmad wani wasa ne wanda kowa kan cire rigarsa, duk wanda yayi kure acikin was an sai a bishi da dukaana cewa ya zagi Ahmad har ya ruga ya kai wani wuri ya duka yana ya tuba,.kila wata rana in rubuto irin wasannin da akeyi a wannan fili da salonsu.
Na zabi wannan filine, saboda a lokaci guda akan iya samun yara masu yawa suna wasa kala kala . A nawa zabin idan na sagar da hannun dan kincimi a wannan fili kowa zaiji labara kuma zan zama gwarzo, kowa zai rika jin tsoro na.
Gab da magariba Dan kincimi yazo har kofar gidanmu yana neman jin ko abin da takule shi dazun da wasa na keyi sai kawai na rika wani cin magani nace mu hadu kawai a dandali in an jima, yana gidanmu har aka kira sallar magriba ya shiga masallacin gidanmu ya yi salla ni kuma na dai daita sahu kusa dashi na taka masa dan yatsa don dai in kara hassalashi,
Tun wuri na isa fili, da laya ta matse a kubakar wando,ga wasa nan anayi hululu kala kala,sai sowa daraha kake ji iri iri,ni kuma ina tunanin cewa nan da wani lokaci zan zama kamar wani sarki a tsakanin yara,zan juya su in sarrafasu sai yadda nayi dasu,zan taka in murje tunda ina da karfi,can sai naji tafiya bayana
Ina juyawa sai naga ashe dan kincimi yake isowa inda nake,kafin ya karasa isowa saina fara tsalle irin yan damben turawa [boxing]yana isowa sai na debo kasa na nuna masa nace gata tsiya gata arziki ya kabe daya sai ya falle tatsiyar. Sai naja baya nashafi layata na nufo shi,zan kai masa bugu da niyyar in ya maido bugun sai hannunsa ya sage shikena abin nema ya samu,
Dan kincimi sai ya cabe hannayen gudaa biyu ya hada su wuri daya ya rike ya danna su kasa ya sa hannunsa guda yayi ta falla mani mari nan na rika ganin wasu irin taurari,san nan narikia jin wani kida maras dadi a kunne na,
Da kyar na kubce,na juya da gudun tsiya,ina gudu sai na fada cikin masau was an way a zagi Ahmad?dai dai lokacin da na shiga an fara bugun wani,sai kawai sukayi tsammanin cikinsu nake sai ji kake tas tas bugu kota ina,nan na kara rudewa na daka da gudun tsiya,su kuma suka ce dawa aka hada mu bada kai ba!
Bugu ko ta ina da haka na kai gidan kakata na fada dakin tan a shige kuryar dakin na kuma sige kuryar gado na yi lamo.kakata ta kalleni tace daga ina nace daga sama.aka jefo ni,Allah jikanta ]ta nufi waje ta iske yan wasa kowa da rigarsa a hannu yana jiran in fito yasha moro ga dankincimi tsaye yana haki.
Tace ya akayi suka ce Ai iya shine ya zagi Ahmad ,tace to kuyi hakuri suka juya suka tafi tana komowa daki ta daga karkashin gado ta ganni duk a rude iadanu na wuri wuri. Tace sunce wai kaine ka zagi Ahmad?nace cikin tsoro da firgici kwarai kuwa har ma na dangwaran masa hanci!na taka kafarsa na murza!iya tace to maganinka kenan !gobe ma ka kuma!