WA ZAI CI SANATA A FUNTUA DA DAURA.?

0

WA ZAI CI SANATA A FUNTUA DA DAURA.?
Sakamakon jin ra ayin jama a
Daga Taskar labarai
Sakamakon da jaridar taskar labarai ta samu na jin ra ayin jama a . A shiyyar funtua da daura ta Dan majalisar dattawa.na nuna ga dukkan Alamu
Bello mandiya shine zai dare kujerar yankin .ana shan wahala wajen tallar shi.amma dalilai da yawa na nuna yana iya cin zaben.
Wadanda jaridar ta tambaya.sun bada amsar zasu iya zabensa ba don shi ba.
Don haka akwai yiyuwar Bello mandiya na iya cin kujerar sanata yankin funtua
A shiyyar daura kuma Ahmad Babba kaita zai iya samun kujerar ba tare da wata turjiya mai tada hankali ba.shima saboda dalilai daban daban da wadanda aka tambaya suka bayyana.
A bincike na jin ra ayin jama a.da jaridar ta gudanar.A sanatocin katsina
Katsina ta tsakiya PDP na iya chanye ta.shine Dan lawan katsina Alhaji Hamisu Gambo
Funtua APC na iya samun nasara, shine Alhaji Bello mandiya
Daura APC nayi chanye ta shine Ahmad Babba kaita.
A yan majalisar tarayya.Akwai kujeru shidda da Tabbas PDP na iya samun nasara yayin da sauran APC zata iya ci gaba da rike su.
Gaskiyar lamari,sai sakamakon zabe ya fita zuwa litinin ko Talata mai zuwa .Allah ka baiwa mai rabo sa a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here