Wada maida yabar abin koyi a harkar yada labarai a kasannan

0

Wada maida yabar abin koyi a harkar yada labarai a kasannan — Hon Bello matawalle

Shu’aibu Ibrahim daga gusau

Gwamnan Jahar Zamfara Hon. Dakta Bello Mohammed MON (Matawallen Maradun) ya bayyana Mal wada maida a matsayin Wanda yabar abin koyi a harkar yada labarai a kasannan.

Wannan bayanin ya fitone cikin wata takarda mai dauke da sa hannun, daratta janar Kan harkar yada labaru, Alh Yusuf Idris, wanda aka rabata ga manema labaru, ya ce gwamnan ya firgita,da ya sami labarin rasuwar Malam Wada Maida, Tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Labaran NAN) har zuwa rasuwarsa, Kuma shugaban kwamitin hukumar.

Gwamna Matawalle ya ce ya samu labarin rasuwan malam wada maida ne a kafofin watsa labarai, inda ya bayyana shi a matsayin haziki kuma jajirtatce a masana’antar watsa labarai a duk duniya tunda shi memba ne a sanannun kafafen yada labarai na kasa.

Ya ce irin gudummuwar da Malam Wada ya bayar ga ci gaba tare da karfafa gwiwa ga dimbin matasan kasar nan a harkar yada labarai ba za a taba mantawa.

See also  Yan sanda sun kama matashin da ake zargi ya yi Ajalin matarsa kan Abinci

Gwamnan ya tuna da kyakkyawan aikin da marigayin ya yi lokacin da ya kasance a matsayin babban sakataren yada labarai ga Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake shugaban mulkin soja.

Bayan ya yi aiki a Hukumar Kamfanin Media Trust kuma a matsayinsa na Shugaba na Kamfanin Jaridar na Daily trust,da kamfanin people Daily, Matawalle ya ce Malam Wada wanda ya mutu yana da shekara 70 ya bar babban abin gado a cikin masana’antar watsa labaru wanda ya cancanci yin koyi.

Ya roki Allah ya ba shi hutu na har abada a Jannatul Firdausi , danginsa Kumar Allah ya basu karfin jure rashin.

Gwamnan ya kuma jinjinawa Shugaba Buhari, tare da yi masa ta’aziyya, da kuma kamfanin yada labarai na NAN, da Media Trust da kuma iyalan people Daily da kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here