WALIMAR KARAMMAWA GA JAMI AN ALHAZAN KATSINA A MAKKA

0

WALIMAR KARAMMAWA GA JAMI AN ALHAZAN KATSINA A MAKKA

Daga Badaru Karofi. PRO

Daya daga Cikin masu Kama ma Alhazan jihar katsina gidaje a Makkah Mr zain ya shirya ma shuwagabanini Alhazan Walimamar cin abinci a gidanshi.

Amirul Hajj Kuma Kakakin Majalisar dokoki ta jihar katsina Hon Abubakar Yahaya kusada shiya jagoranci Sauran kwamitoci zuwa Walimar.

Daya ke bayani a gurin taro Walimar Hon. Abubakar Yahaya kusada ya Kara jawo hankalin shi da ya Kara azama Wajen sama ma Alhazan jihar katsina gidaje masu inganci a Makkah yayin Aikin Hajjin.

Ya Kuma yi godiya ga Abinda ya yi masu sannan ya Kara yaba mashi a kan gidajen da ya sama ma Alhazan jihar katsina musamman a Wannan shekarar.

Daga karshe a madadin gwamnatin jihar katsina karkashin jagorancin gwamnan Alhaji Aminu Bello Masari Dallatun katsina Amirul Hajjin ya tabbatar ma Mr zain din da cigaba da bashi goyon Baya domin ganin ya cigaba da samama Alhazan masaukai masu inganci a kawace shekara.

See also  Ba Na Jin Dadin Rayuwar Duniyar Nan, Ina Fatan Na Cika da Imani Ne Kawai, Inji Dantata

Shima a takaitaccen bayanin shi Mr zain ya godema gwamnatin jihar katsina akan damar da ta bashi domin sama ma Alhazan jihar katsina masaukai a Makkah.

Ya Kuma kara Godiya ga dukkan jami’an da suka Halarci walimar cin abinci ya Kuma yi alkawalin cigaba da kokarin ganin Alhazan jihar katsina sun sami masaukai masu inganci musamman a Birnin Makkah.

A Cikin wadanda suka Halarci walimar sun hada da tawagar Amirul hajji da ta board chairman Alhaji Salisu Ado Shinkafi Bunun katsina da Kuma shuwagabanini Sassa na Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar katsina karkashin Babban Darakta Alhaji Muhammadu Abu Rimi (min)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here