Wanda Aka Sace A Batsari Ya Kubuto Bayan Kwanaki Hamsin da Daya….
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina City News
A ranar juma’ar da ta gabata ne, wani mutum mai suna Malam Babangida, mazaunin kauyen Dan-Burau dake cikin yankin karamar hukumar Batsarin Jihar Katsina. Ya Kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane, bayan ya kwashe Kwanaki Hamsin da daya a hannun su.
A zantawarmu da shi, ya bayyana cewa tun a cikin watan uku na shekarar nan, yan bindiga suka afka gidan shi, suka yi awon gaba da shi, tare da madakin shi. Wadda cikin iKon Allah suka sake ta tun ba a nisa ba.
Yayin da suka yi dawan Zamfara da shi, inda suka dunga gana masa azaba ta hanyar duka da hana shi abinci. Bayan kwana biyar a samu kafar tsirewa, amma hakar shi bata cimma ruwa tun bai yi nisa ba, suka kamo, wahalar ta koma sabuwa.
Babangida Dan-Barau ya kara cewa ya zauna karkashin Daba uku, wadda ya kyautata zaton ana bayar da shi sari ne ganin ya yi nauyin kasuwa, ga kuma ya neman tserewa.
Ya dai samu kubuta a dabar karshe da ya zauna, inda ya shafe Kwanaki uku ya gudu da boya cikin geza tare da cimmar madin kanya in an yi karo da ita da Dan ruwa da ya kwanta a kan hanya. Duk da haka ya samu taimakon wani Bafillatani gab da zai shiga gari, da ya dauke shi ya Kai shi gida ya ciyar da shi, tare da bayar da umarnin a kawo shi garin Dumburawa inda aka nema masa taimakon kawo gida a cikin iyalansa.
Jaridun Katsina City News, suna wa Babangida Allah ya kiyaye gaba, da fatan Allah ya kawo wa jiharnu da kasarmu zaman lafiya.