WANE SARKI NE BAI SHIGA SIYASA?

0

WANE SARKI NE BAI SHIGA SIYASA?

Sharhin Taskar labarai

Ana ta rubutu da magana cewa wai sarkin Kano Sanusi ya shiga maganar siyasa? Tambaya wane sarki ne bai shiga siyasa?

A tarihin Kano kowa ya san marigayi Ado Bayero sun yi tsama da gwamnan Kano Rimi har Rimi yayi yunkurin cire shi har aka yi tarzomar da aka kashe sakataren gwamnatin lokacin.

A Kano kowa ya san goyon bayan marigayi sarkin Kano ga Shekarau ya sanya yayi mulki zango biyu a jere kowa ya san yadda daga fada ake juya gwamnatin Shekarau.

A Katsina sarkin Katsina Abdulmumini Muhammadu Kabir Usman ya taba cewa in Shema yaki yarda ya sake tsayawa takara a karo na biyu zai kai shi kotu. A taro wajen bude makarantar horas da jami’an tsaro na farin kaya ya fadi haka.

A Legas Oba na Legas ya taba cewa, Idan Inyamurai na jihar suka juya ma APC baya. zai kora su har cikin teku wanda aka yi ta rubutu akan lamarin, su ka ce ya fito ya basu hakuri yace bai yi.

See also  El-Rufai da sabon Sarkin Zazzau na Shirin Cire Masu Zaɓen Sarki Guda Hudu

A Sokoto an danganta Sultan da goyon bayan Aminu Tambuwal, wanda har ‘yan APC suka rika waka suna cewa sabon gwamna da sabon sarki.

A zariya Makarfi ya zargi sarkin Zazzau wanda har aka taba walakanta Makarfin a wani taron sallah haka kuma El-Rufai ba irin cin kashin da bai yiwa sarkin na Zazzau ba.

Misalan na sarakuna da garuruwansu suna da yawa, amma mun kawo kadan don tattaunawa.

Matsalar sarkin Kano biyu ce, ko uku na farko ba munafukin sarki bane, yana fadin zuciyarsa ga bakinsa.

Ta biyu ‘yan PDP ba su yafe masa ba, yana cikin wadanda ya karya su da bakinsa da tone tonensa.

Na uku ‘yan APC basu sonsa don yana fadin gaskiyar fahimtarsa akan gwamnatin su wanda maganar ba tayi masu dadi don haka yana da zunubi a wajensu.

Shiga siyasa ga sarakuna dole ne, kodai a munafunce ko a bayyane don haka a bar shiga hakkin sarkin Kano ace wai ya shiga siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here