WANI DAN BAIWA YA BAYYANA TSAFE JAHAR ZAMFARA
Daga Taskar labarai
Wani yaro Wanda Allah yayiwa baiwar bayar da maganin bindiga kuma a gwada taci, ya bayyana a wani kauye mai suna Tsauni,kusa da garin yan kuzo ta karamar hukumar tsafe jahar zamfara.
Yaron mai kananan shekaru,Wanda ake jin Aljannu ke bashi maganin ,yana badawa Akan naira dari biyar kacal.kuma zai ce ka hadiye nan take.
Ance yana daga hannunsa da kwarya,sai kwaryar ta cika da maganin sai ya rika bayarwa.dan baiwar yace, Allah ne ya sahale masa don jama a su samu kariya daga harin da mahara kan masu suna kashe su.
Ance ko mugu yaje wajensa,sai ya gane shi,baya bashi.
A jiya laraba wakilan taskar labarai sunje garin inda suka iske sama sa mutane dubu Akan layi.
Ko motoci sunkai dari biyu.wasu na kwanaki.a layi
Da mahaifin yaro yaga,na nesa na wahala ,sai ya tsara wani tsari,na yan nesa na iya turo mutum daya yazo ya samar masu Rana. Wadda da sunzo.ba bata lokaci za a gansu.
Jaridar taskar labarai, tayi hira da mahaifin yaro Wanda zamu kawo maku cikakkiyar hirar nan gaba.
Maganin an na bindiga an gwada an gwada kuma taci sosai.in mutum akayi masa harbin farko Zara tashi.amma ba abinda zai same shi.in aka sake harbawa bata tashi.in aka harba na uku..zata lalace kwata kwata.
Jaridar taskar labarai tayi hira da mutane uku da suka ga Dill a lamarin.
Munyi kokarin daukar hoton layin jama a suka ki,yarda sai uban yaron yace tun mutane basa so.to kar a dauke su hoton.