WANI DAN KATSINA YA ZAMA DAN MAJALISAR TARAYYA A KANO.
daga taskar labarai
Wani matashi dan Asalin jahar katsina ya chanye kujerar Dan majalisar tarayya a mazabar ungogo.da minjibir a jahar karkashin tutar jam iyyar APC a jahar Kano
Zababben dan majalisar tarayyar mai suna sani ma aruf mai wake .mahaifinshi Dan kauyen na sarawa ne a karamar hukumar kankia , Wanda yaje Kano sana ar sayar da hatsi a kasuwar dawanau.ana kiransa da Alhaji ma aruf mai wake..Alhaji ma aruf kanene ga Alhaji mani nasarawa, Wanda yayi takarar sanata shiyyar daura a jam iyyar PDP.kuma a farkon satin nan ya koma APC.
Mahaifinsa ya rasu shekarar 2003 sai yake zaune wajen danginsa dake kano,ya Shiga siyasa.kuma ya samu nasibi acikinta.
Tun a zaben fitar da gwani, an rika masa yarfen ba Dan asalin Kano bane.amma ya rika bada martanin cewa .shi musulmi ne.hausa fulani.kuma daga katsina. Wanda kamar yan tagwaye ne.da Kano.yace tabbas kasuwanci ya kawo uban sa.kano.amma ya cika duk kaidar da dokar kasa ta bashi.na zama Dan Kano asalinsa daga katsina.
Kyawawan halinsa.yasa,mutanen mazabarsa suna sonshi. da gumu tayi gumu.ana yarfen siyasa.magoya bayansa suka chanza salonsu na kamfen .suna cewa..sai Dan Dan katsina mutumin kirki.
A yakin neman zaben an buga sosai.amma a zaben .ya canye da tazara mai yawan gaske.