Wani Deliget Din Apc Ya Rasu A Abuja

0

Allah ya yi wa mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta tsakiya, Alhaji Isah Baba Buji rasuwa a Abuja. Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC na jihar, Bashir Kundu ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ta wayar tarho.

Yace marigayin wanda kuma wakili ne a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja. Rahoto ya ce marigayi Baba Buji ya kwanta da safe a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa a lokacin da yake shirin zuwa wurin da za a gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC.

See also  2023: PDP ta rasa mambobi 1,500 da Suka canza sheƙa zuwa APC a Jigawa

“Ya fadi a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti ya mutu kafin ya isa asibitin. Da muka isa asibiti an tabbatar da rasuwarsa”.

A cewarsa, Marigayi Mataimakin Shugaban ya rasu ne sakamakon ciwon zuciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here