Wannan shine malam Bisallah da ‘yan ta’@dd@n daji suka cirewa hannuwa duka biyun a ƙauyen Wadu ƙauran Namoda Zamfara State.

0

Yadda abun ya faru yace ‘yan ta’addan bayan duk wani ta’addanci na cin zarafi da suke zuwa su masu, tuni dama sun kwace masu shanun huɗa na yau da gobe,. Sun ƙwace masu tumakan su kaf, sun dawo sun sake kwashe ƙadduwowin ƙauyan gaba ɗaya, shine suka sake dawowa su kwashe masu kajin ƙauyen shine ran malam Bisallah ya ɓaci yakasa jurewa bayan masu bindigar sun wuce sun bar masu addina da sanduna sai yace masu “wai ya kuke so musaka kanmu ne! Wannan wacce iriyar baƙar azaba da horo kuke mana? Laifin mai mukayi maku haka?.

Nan take ɗayan su yace mai suke jira dashi? Tofa shine suka yimai wannan hukunci sakamakon maganar daya masu, akwai kanin sa shima sun kashe masa hannu ɗaya akokarin sa na ceton yayan nasa bayan yakasa jurewa cin zarafin daya ga suna yi masa.

See also  Kanfanin KEDCO Ya Nemi Afuwar Abokan Huldarsa Kan Karancin Wutar Lantarki

Ahalin yanzu dai shi wannan bawan Allah sun gama na kasa masa rayuwar sa karfi da yaji bayan rusa masu tattalin arziki da sukayi.

Ku taumaka mana da SHARING ko Allah zaisa sakon ya isa ga mahukunta ayankin su ɗan taimaka masa domin kuwa ayanzu ga Nauyin iyali kuma babu komai sun ƙwace masu.

Source: Gimbiya FM

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here