WASIKA GA GWAMNAN KANO AKAN MASARAUTAR KANO.
Daga Danjuma katsina.
Bayan gaisuwa da girmamawa na rubuto maka wannan wasika ne, don shaida maka tunanin al ummar dake wajen kano akan abin dake faruwa a kano tsakanin gwamnatinka da masarautar kano.
Da farko ina son ka sani kano cibiya ce,ta duk wani hausa/fulani dake duniya.cikin hausa/fulani goma na duniya.biyar nada alaka da kano kota auratayya, jini,asali ko kasuwanci kowata hudda mai karfi.
Duk jihohin dake da makwabtaka da kano suna da alaka ta kut da kut da kano ta daya daga abin da fada a baya.misali a jaha ta katsina.yankin sanatan funtua.mafi yawansu asalinsu kanawa ne.haka yake a yankin sanata ta mazabar daura,hatta katsina ada tana karkashin kano ne a zamanin mulkin turawa.
A katsina ta tsakiya,kusan gida takwas cikin goma nada wata alaka da kano,ta auratayya,jini,asali, ko kasuwanci ko wata hudda mai karfi .ni marubucin nan tsatso ne daga jinin zuriyar Malam muhammadu bakatsine,da yar uwarsa malama jibado.wadanda katsinawa ne a asali amma dasu akayi jihadin shehu usman dan fodio a kano.kuma sun taka rawa sosai kamar yadda tarihi ya tabbatar.
wadannan dalilai suka sanya,duk abin da ya shafi kano duk duniyar hausa/fulani kan amsa.kuma yakan zamar kamar amo ko ina kaji ya dauka.akan shiga damuwa akan lamarin sosai.
Yallabai, kana bani tausayi, don ana misalta ka da mutumin kirki, mai hakuri wanda miyagun mutane ke sarrafawa.don haka wani lokaci sai ka dau matsayi bisa kuskure a lokacin da bai dace ba.sai ka zama baka da goyon baya .
Rabuwarka da kwankwaso,an dauka kaine kayi butulci.don kwankwso ya kasance tare da kai a duk tsawon zamanku shekaru takwas yana rike da mukamai baku da gwamnati a kano.
kayi ta daukar matsaya na tafiyar da mulkin kano.wanda sukayi ta jawo maka karin bakin jini ga duk wani mataki daka dauka, misali gina shaguna a filin idi,da ginin gadar kasa a hanyar zariya.
Hoton bidiyon da ake zargin kaine, inda wani mutum na saka dalar amurka a ljifun babbar riga,da hana binciken don tabbatar da gaskiyar hotunan ya sa alamar tambaya da yawa akan ka.
fara daukar mataki akan masarautar kano a cikin watan ramadan wanda ya dagawa duk musulmin duniya hankali ya kuma zama abin magana a wannan wata mai alfarma.wannan ma ya jawo maka bakin jini ba dan kadan ba.
A takaice yallabai,abin da gwamnatinka tayi akan masarauta a cikin azumi ya dagawa musulimi duniya hankali a wannan wata mai alfarma.
Duk wanda ke bin yadda lamurra ke gudana na tsakanin gwamnatinka da masarauta, yasan ba iklasi a ciki sai dai wani aiki don huce takaici wanda wasu ke zugawa ana yi.
Duk kuma abin da ba Allah bane asalinsa baya dorewa ko ba jima ko ba dade, babban abinda ya kamata mutum ya fara kawowa a gabansa ga duk abinda za fara shine Tarihin da zai bari, wanda kuma zai rika binsa da farautarsa ko bayan ransa.
Wace nasara aka samu da matsayar gwamnatin kano ga masarauta? Rarraba kan Al umma daya mai karfin gaske,wadda ke magana da murya daya ada.
kashe dimbin kudade don gaisuwa da wayar da kan mutane akan matsayar da gwamnati ta dauka akan masarautar,wanda duk mai bin shirye shiryen rediyo da sauran kafofin sadarwa yasan ana kashe kudaden da ya kamata a saka su wani wajen da ya dace.
kashe kudade,don kawai a inganta sabbi masarautun, wadanda ya kamata a saka su wasu ayyukan gina Al umma da yafi dacewa.
Dauke hankalin al ummar kano daga gaskiyar abinda ke ci masu tuwo a kwarya zuwa tattauna abin da inda zai amfani rayuwarsu kai tsaye.
Duk a wannan ba inda talaka sai amfana, sai dai ranar hawa na sallah karama da Babba ayi a inda ya fito sai kuma ranar jumma aje sallah da kuma zaman fada.
saboda kowa yasan cewa, a mulkin dimokaradiyya.kansila,ciyaman, dan majalisar jaha, na tarayya da sanata.sune kai tsaye suke magana akan al ummarsu ba wani sarki ko wata sabuwar masarauta ba.
yallabai, wata rana zaka bar mulkin kuma bayan nan Allah masanin wa zai amshe ka,kuma miye tsarinsa.A lokacin duk masu zuga ka zasu guje maka.
wannan abin da ake wata Rana kai zata dawo maka da iyalinka.kai ne za ai ta kawo tarihi ana danganta shi da akai , a alokacin kowa zai juya maka baya yana fadin cewa kai ne ka sanya shi.
yana da kyau a saka hangen nesa. a kuma sanya kula komai mutum zai gabatar ya tuna cewa wata rana ya abin zai dawo masa kuma ya zama mai tuhuma, mai bada shaida kuma alkalin kansa da kansa.
akan bincike na masarauta, a wannan zamanin da muke a ciki wanene za a bincika ya tsallake ba a same shi da laifi ba.? wata rana zaka bar mulkin kana fatan ayi in maka binciken kwakwaf?
bincike,don bata suna bai hana abin da Allah ya tsara bawa zai yi nasara akan su na Rayuwa.misali zamanin Abaca na shugaban kasa, ya sanya anyi wa tsohon gwamnan kano kabiru gaya binciken terere.wanda aka rika yada abin a gidan rediyo kai tsaye da bada labarin sauran kafofin watsa labarai.yanzu kabiru gaya sanata ne, daga jahar kano a karo na uku.
ina rokon a sa hankali,lura da hangen nesa.don gaba don wata rana.ko don zuriya da iyali.da sauran al umma.
DANJUMA KATSINA.
Mawallafi ne kuma Dan Jarida.
ana iya samunsa a: mdanjumakatsina@gmail.com
08035904408