Wasu makarantun sakandare 23 a Zamfara na bukatar dauki cikin gaggagawa

0

Wasu makarantun sakandare 23 a Zamfara na bukatar dauki cikin gaggagawa

Shuaibu Ibrahim daga Gusau

An bayyana cewa gwamnatin jihar zamfara ta gano makarantun sakandare 23 da ke bukatar daukin gaggawa .

Hakan ya fitone daga bakin Kwamishinan Ilimi na jihar zamfara, Dakta Ibrahim Abdullahi a lokacin da ya kira taron manema labaru a ofishinsa a ranar Juma’a yayin da yake tsokaci kan wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo
kan makarantar sakandare ta Gwamnati da ke karamar Hukumar Shinkafi a jihar.

Kwamishinan ya ce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Shinkafi na daya daga cikin makarantun da suka lalace wadanda gwamnatin ta gada daga tsohuwar gwamnatin Abdul’aziz.

Abdullahi ya kara da cewa, an dauki hoton bidiyon ne don sanyawa gwamnati ta hanyar bata mata suna, Kwamishinan ya ce gwamnati ta riga ta tantance yanayin dukkanin makarantun firamare da sakandare na jihar tare da gano makarantu 23 ciki har da na Shinkafi, wadanda ke bukatar a hanzarta gyarasu don a ci gaba da amfani dasu.

See also  Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Ministoci Ranar Litinin

Ya ce bayan na hau Wannan mukamin Kwamishina na Ilimi, na zagaya dukkanin makarantun da ke fadin jihar zamfara, na ga halin da makarantunmu suke ciki, da kuma makarantun da Wannan gwamnati ta gada daga gwamnatin baya.

Ya ce Wannan shine ne ya sa Gwamna Bello Muhammad Matawalle kansa ya zaga cikin jihar tare da duba yanayin makarantun firamare da sakandare.

Ya Kuma bayyana cewa da a ce wanda ya fito da wannan faifan bidiyon ya ziyarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Tsafe, da zai ga yadda makarantun suka lalace wanda muka karba daga tsohuwar gwamnati.

Kwamishinan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, gwamnatin jihar za ta ba da kwangila don sake gina makarantun da suka lalace a fadin jihar.

Ya yi kira ga jama’ar jihar da su yi amfani da hanyoyin da suka dace don ba da shawara ga gwamnati, kan hanyoyin bunkasa jihar maimakon sukar da ake yi ta siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here