WATA CIBIYA TA KARRAMA SHUGABAN JAMI’AR NOUN FARFESA ABDALLAH UBA ADAMU

0

WATA CIBIYA TA KARRAMA SHUGABAN JAMI’AR NOUN FARFESA ABDALLAH UBA ADAMU

Cibiyar wanzar da zaman lafiya da Dabbaka Sasanci ta karrama shugaban Jami’ar Karatu daga gida Farfesa Abdalla Uba Adamu.

Wannan karramawar ta zo ne bayan kammala taron cibiyar na shekara-shekara karo na sha biyu a harabar hedikwatar Jami’ar NOUN da ke Abuja.

A lokacin da daya daga cikin membobin kwamitin amintattu na cibiyar na jawabin bankwana a wajen taron Farfesa Isaac Oluwole, ya tabbatar da karramawa a matsayin abin da ya dace, duba da irin gudumuwar da shugaban jami’ar ke bayarwa wajen dorewar zaman lafiya a wannan kasa.

Sannan sun yaba da irin yadda shugaban Jami’ar ya amince da gudanar da taron na kwana uku a hedikwatar Jami’ar da ke Abuja.

Taken taron na bana dai shi ne, kaluballen da ke tattare da sasanci da kuma yadda za a gina zaman lafiya a Nijeriya”

See also  Tinubu Zai Taimaka Wajen Hako Danyen Mai da Ake da Shi a Arewa 

A lokacin da ake tabbatar da karramawar shugaban kwamitin Amintattu na cibiyar Farfesa Suleiman Bogoro ya bayyana muhimmancin gudanar da taron a Jami’ar, musamman saboda irin gudumuwar da Jami’ar ke bada wa a fannin.

Lokacin da ya ke amsar Karramawar Shugaban Jami’ar Farfesa Abdallah Uba Adamu ya nuna jin dadinsa da kuma tabbatar da cewa Jami’ar zata duba yiwuwar bude wata cibiya kan abin da ya shafi zaman lafiya a cibiyar Bincike ta Olusegun Obasanjo da ke Jami’ar.

Fafesa Abdallah ya bayyana cewa kwas din Sassanci da zaman lafiya da kuma kwas din Koyon sana’o’i sune kwasakwasan da suka fi samun yawan dalibai a Jami’ar.

Lokacin da Magatakardan Jami’ar Mista Felix Edoka ya ke bayanin godiya ya bayyana cewa, wannan karramawa ba Farfesa Abdallah kadai aka yi wa ita ba har da ma Jami’ar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here