WAYA KONA MOTA A CHARANCI?
……A hanyar zuwa bada tutar APC
……Rikicin Gidan siyasa ne?
Muazu hassan
@ katsina city news
A yau Alhamis 31/3/2022 aka Kona wata mota Mai dauke da Hoton tallar kamfen din Mustafa inuwa.
Lamarin ya faru da misalin da karfe sha daya na Rana a gaf da isa kasuwar charanci, cikin gari charanci.
Ganau da wakilanmu sukayi magana dasu,sunce babu Wanda zai iya cewa ga yadda wutar ta faru.
Wani binciken da jaridun mu sukayi sun gano akwai yiyuwar rikicin bangarori biyu na gidan takarar Mustafa inuwa ne.zawiyyar Alheri da Alheri Danko ne.
Binciken mu ya gano cewa, Daya daga cikin jigo a kamfen din Mustafa inuwa inuwa mai suna Hamisu Hara shugaban kungiyar Zawiyyar Alheri.kungiyar da ta fara tallar takarar Mustafa inuwa sama da shekaru biyu da suka wuce.
Hamisu hara yana tsaye tare da wasu motocin sa a wajen garin katsina.
Suna jiran sauran abokan tafiyar su suzo a tafi.sai ga wasu matasa da da mota da kuma rigunan.Alheri Danko ne, wata kungiya ita ma mai kamfen din takarar Mustafa inuwa.
Ganau sun tabbatar mana, sai wadannan yan Alheri Danko ne, suka gabatar da kansu ga Hamisu Hara.suka kuma nemi,ya basu wani abu.Hamisu Hara ya amsa masu zai basu amma sai an dawo taron kankia.
Ganau a tawagar Hamisu Hara, sun fada mana cewa,wannan mota ta da ake tsammanin ta yan Alheri danko ne.
Sune suka rika gifta motocin Hamisu Hara har suna gugarsu.
Ganau suka ce, wata gilmawa da gugar da waccar motar tayi ma wannan bas din, sai kawai aka ga wuta na tashi.
Wasu na zargin daga waccar motar aka Jefo wani abu ta fada kasan motar su Hamisu Hara sai kawai wuta tashi.
Mutanen gari da kansu suka zo sukayi kokarin ture motar da yunkurin kashe wutar.amma sai da ta Cinye motar kamar yadda Ganau suka tabbatar mana.
Wadannan da ake zargin yan Alheri Danko ne, Basu kyale Hamisu Hara ba.sai da suka bishi har wajen taron a garin kankia, sukayi fara bugunshi, Allah ya Sanya jama a suka kwace shi.
Ganau sun tabbatar mana,cewa ,sunga lokacin da matasan suka zo suna zagin Hamisu Hara,suna cewa.wai yayi masu Sharri wajen sakataren gwamnati Mustafa inuwa yace,da suka je Abuja barci sukayi.
Daga nan Daya ya Keta masa Riga ta Dire har kasa.wasu kudi dake jikinsa duk suka wasashe.
Ganau sun ce,har direban motarsu sai da yazo yace ku bar bugunshi.ance ne ku ja masa kunne da gargadi,ba ku buge shi ba.
Ganau sun ce daga nan aka Sanya Hamisu Hara a mota aka dawo dashi katsina.
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245