WAYE YA KIRKIRI TUTAR NAJERIYA?
_Muhammad Bala Garba, Maiduguri._
Tabbas tarihin Najeriya baya kammaluwa ba tare da an ambaci sunan dattijon arzikin nan da yayi anfani da basirar sa ya dauki tsawon lokaci sannan ya kirkiro tutar Najeriya da yanzu haka ake anfani da ita.
Tarihi dai ya nuna cewa tutar ta Najeriya dai wani bawan Allah ne mai suna Mista Michael Taiwo Akinkunmi da ke da shekaru 23 kacal a wancan lokacin ya kirkire ta a shekarar 1958 kafin daga bisani a amince da ita sannan a kaddamar da ita a ranar 1 ga watan Oktoba shekara ta 1960.
Gabanin Najeriya ta samu ‘yan cin kanta a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, kasar na amfani ne da tutar Birtaniya a karkashin gwamnatin turawan mulkin mallaka na Ingila.
Har sai a shekarar 1958 lokacin da ake shirye-shiryen mika mulki ga ‘yan Najeriya aka fidda sanarwar gasar zana tutar kasar. Jama’a da dama sun shiga gasar, inda kowa ya tura irin nasa zanen.
A wannan lokacin Taiwo Akinkunmi dalibi ne dake karatu a Kwalejin fasaha ta Norwich dake Ingila, ya shiga gasar, inda ya tura zanen sa zuwa Legas kuma bayan tantance zanuka kimanin 2,800 na wadanda suka shiga gasar, a karshe aka zabi ta sa mai launin Kore da fari da kore.
Sai dai kuma asalin zanen da ya aike na dauke da hotan rana a kan farin, wanda alkalai suka cire a lokacin.
Kuma a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, ranar da turawa suka ba Najeriya ‘yancin kanta aka daga tutar da Micheal Taiwo Akinkunmi ya zana wato mai launin Kore da Fari da Kore, yayin da aka sauke tutar Ingila.
Ma’anar launin koren dake jikin tutar Najeriya shine Noma, wato hakan nan nufin Allah ya albarkaci Najeriya da kasar Noma, yayin da launin farin ke nuni da zaman lafiya a kasar.
Turawan da suka mika mulkin ga gwamnatin Najeria a wannan lokacin sun ba Micheal Taiwo Akinkunmi kyautar pan 100 na Ingila.
An haifi Micheal Taiwo Akinkunmi a ranar 10 ga watan Mayu a shekara ta 1936 a garin Owu a jahar Ogun. Ya yi karatun furamarensa a makarantar Baptist Day Secondary Ibadan, ya yi kuma karatun sakandirensa a Ibadan Grammar School, ita ma a garin na Badun.
Daga nan ne kuma ya samu aiki a a sakatariyar gwamnati ta Ibadan, inda yai aiki na tsawon wasu shekaru, daga nan ne kuma ya ta fi Ingila karo karatu a kwalejin fasaha ta Norwich, inda ya karanta fasahar noma.
Mista Akinkunmi ya koma Najeriya bayan da ya kammala karatunsa, inda ya kama aiki a ma’aikatar ayyukan gona.
Yayi ritaya daga aikin gwamnati amatsayin mataimakin Darakta.
A shekarar 2014 Gwamnatin shugaba Jonathan ta karrama shi da kyautar girmamawa.
Sai dai kuma yanzu yana nan talauci yayi masa katutu, domin gwamnati tayi watsi dashi.