YA KASHE SAMA DA NAIRA MILLOYAN 43 A TALLAFIN AZUMI A JIHAR KATSINA.
@ jaridar taskar labarai
shugaban Bankin bada lamanin kudaden gina gidaje ga ma’aikata na Gwamnatin Nigeria Arc Musa Ahmed Dangiwa ya raba kayan azumi ga al’ummar jihar Katsina wanda kudaden su ya kai naira milliyan 43
Shugaban kwamitin raba kayan Hon. Salisu Hamza Rimaye wanda kuma shine Danmajalisa me wakiltar karamar Hukumar Kankia a majalisar dokokin jihar Katsina yace daga cikin kayan da aka ra ba akwai gero buhu 1064 da buhun shinkafa 720.
Shugaban kwamitin raba kayan yace an raba kayan a shiyyoyi uku na Danmajisar Dattawa dake jihar Katsina inda kuma kowace shiyya karamar Hukumar ta zata samu buhu 50
Haka kuma Danmajalisar ya kara da cewa Akwai kudade da Dangiwa yaba shugabannin Jam’iyyar APC na jaha da na shiyya-shiyya da kananan hukumomi a jihar wanda adadinsu ya kai naira milliyan uku.
Dalilin bada kayan a cewar Hamza dan tallafa wa al’umma a wannan lokaci na azumi wanda dama halin Ahmed Dangiwa ne tausayawa al’umma.
An dai kaddamar da bada kayan shiyyar Daura a birnin Daura, sai na shiyyar Katsina a cikin garin Kurfi, ya yin da aka kaddamar da na shiyyar Funtuwa a garin Musawa.
Daga karshe dan majalisar ya yi yakinin cewa dukkanin wadanda aka ba tallafin suma zasu tallafama al’ummar kusa dasu.
Da yake magana a madadin wadanda suka amfana da tallafin mataimakin Shugaban jam’iyar APC a shiyyar Funtuwa Bala Abubakar Musawa ya godewa Musa Ahmed Dangiwa game da hangen nesan raba wadannan kaya. Inda yace raba kayan yazo dai dai lokacin da ya dace kana ya yi fatar Allah ya sakawa Dangiwa da alkairi.