YA RATAYE KANSA BAYAN YA FASA WAYARSA TA SALULA, KUMA YA TAUNE LAYIN WAYAR.

0

YA RATAYE KANSA BAYAN YA FASA WAYARSA TA SALULA, KUMA YA TAUNE LAYIN WAYAR.

Al’ummar kauyen Ikot Akpan, Afaha Obong dake yankin laramar hukumar Abak ta jahar Akwa Ibom. Sun shiga rudani bayan sun wayi gari da ganin gawar wani mutum rataye a bishiya tana lilo. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutum da aka sakaya sunansa dan asslin kauyen ne wanda yakan fita zuwa wani gari mai suna Oron domin gudanar da sana’arsa. Jefi-jefi yakan dawo kauyen nasu ya yi kwanaki a gidan wani kawunsa kafin ya sake komawa garin da yake kasuwancin nasa. Domin ba shi da gidan kansa a kauyen.

Bincike ya bayyana cewa, wannan mutum ya yanke shawarar ya datse rayuwarsa ta hanyar rataye kansa a bishiyar.Kafin hakan kuma, sai da ya fasa wayarsa ta hannu, sannan kuma ya taune layin wayar tasa.

See also  SANATA KATSINA TA TSAKIYA, WA ZAI KAI LABARI.? BARKIYA KO DAN LAWAN.?

Duk da dai har yanzu tsakanin dangin mutumin da kuma jami’an tsaron yankin ba wanda zai ce ga dalilin da ya sa ya zabi ya kashe kansa ta hanyar rataye kansa a bishiyar dake kofar gidan kawun nasa, inda ya saba sauka idan ya zo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here