YADDA AKA SACE MATAR MATAIMAKIN BABBAN AKANTA JANAR NA KATSINA

0

YADDA AKA SACE MATAR MATAIMAKIN BABBAN AKANTA JANAR NA KATSINA
Daga Taskar labarai
A daren laraba ne 28/ 10/2019 wasu mutane suka je unguwar manyan ma aikata da masu galifu na katsina suka tafi da matar Alhaji sani Bk mataimakin babban akawunta janar na jahar katsina.kuma madakin majidadin sarkin katsina.
Taskar labarai taje gidan da jijjifin safiyar Alhamis domin jin ya wannan masifar ta faru.? Mun iske gidan cike da masu zuwa jaje.kuma yaran gidan wadanda abin ya faru a gabansu sunyi mana bayani dalla dalla.
Daya daga cikin su ya shaida mana cewa, muna a wajen gida zaune muna sha iska.sai ga wata mota 206 ta zo ta Dan tsaya ta fito daga gabas sai tayi yamma.
Mun dauka ma mai gidan ne,don da 206 ya fita a ranar,har mun Mike tsaye sai muka ga ta wuce , mu ka dawo muka zauna .
Can sai ta dawo daga yamma ta nufi inda ta fito.watau ta gabas.tana wuce sai kawai ga wasu mutane sun shigo gidan a guje kowa da bindiga a hannunsa suka ce duk mu kwanta.
Sai suka nufi cikin gidan.daya da yaso yayi gardama nan suka buge shi da bakin bindiga ya some.
Wani cikin yaran yace an hadu dashi a hanyar shiga gidan aka cakumi rigarsa.aka ce ya shige masu gaba.suna tafiya suna cewa wajen hajiya karama suka zo.nan sai nace a duk gidan babu hajia karama.sai suka buge ni a kafada da gindin bindiga.
A cikin falon gidan sun sa kowa ya kwanta.suka bi fuskokin Matan suna dubawa.suna cewa hajia karama muke nema.
Duk wadda suka duba fuskarta sai suce ba ita ba. Ita kuma wadda suke neman wadda ba Wanda ya San wa suke nufi.tana can wani bangaren gidan sai taji hayaniya sai ta fito da sauri tace minene ke faruwa ?
Sai sukace yawwa, dama ke muke nema don haka suka Sanya ta a gaba suka tafi da ita. Suna tafiya aka shaida ma jami an tsaro cikin mintoci kadan suka cika hanyar zuwa gidan
Yaran gidan sun shaida ma taska labarai cewa, mutanen sun fi Goma.kuma duk fiskarsu a bude take in banda daya da ya rufe fiskarsa kuma shine yake ma sauran jagora.
Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin kuma suna a akan bincike da hadin gwaiwar sauran hukumomin tsaro.
________________________________________________
Taskar labarai da yar uwarta The links news jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta na zamani
Suna a shafukan www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com,.lambar waya Kira ko whazzap 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here