Yadda Aka Yi Wa Kalaman Shugaba Buhari Mummunar Fahimta Kan Matasa

0

Wasu ‘yan Nanjeriya na cigaba da fassara kalaman Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta hanyoyi daban-daban, yayin da wasu mukarraban shugaban kasar suka ce an yi mummunar fahimta game da kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa mafi yawan matasan kasar ci-ma zaune ne, sun fi son su ci daga sama.

Shugaba Buhari yana magana ne a taron kasashen renon Ingila dake gudana a birnin Landan.

Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a tsakanin matasan kasar musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan kalaman da suka ce na zubar da kima ne, da shugaban ya yi.

See also  BREAKING: Buhari’s gov’t bans sim card importation

Jim kadan, mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai Sha’aban Sharada, ya ce matasa da dama ba su fahimci kalaman Shugaba Buhari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here