YADDA AKE TSARE DAMU: INJI MASU CORONAVIRUS A KATSINA.
~~~~~Hira da wadanda ke jinyar ciwon. “Yadda aka kawo mu, halin da muke ciki”
Jaridar Taskar Labarai ta samu zantawa da wasu da ake tsare dasu suna jinyar cutar Coronavirus a nan Katsina.
Mun yi magana dasu ta waya, kuma mun sakaya sunayen su, da inda suka fito amma mun fadi labarin su kamar yadda suka shaida mana.
Daya daga cikin su wanda muka sa masa lakabin Malam A. Dan shekaru 43. baya da wani ciwo dake jikinsa, ya shaida mana cewa, “ni ina sana’ar shanu ne a Legas, da aka fara wannan yanayin sai na biyo wani da yaje can sana’a muka dawo tare.
Ina gida aka ce mani wancan ya kamu, aka zo gida aka yi mani tambayoyi don wai mun taho tare da shi a mota.
Kwatsam wata rana aka bugo mani waya aka ce in samu babur ya kawo mu Dutsinma.
Muka zo aka ce za a debi samful namu akai Abuja a gwada, bayan an diba aka ce mu koma gida, ranar nan kawai sai ga motocin Jami’an tsaro da na asibiti har garinmu wai an zo tafiya damu muna da cuta. Jama’ar gari suka ce basu yarda ba, da muka ga za ai ba kyau muka ce su tafi zamu kawo kanmu.
Muka ba mutane hakuri, muka sake daukar babura muka kai kanmu muna isa aka gewaye mu kamar masu laifi, nan muka fara ganin kyama, aka kawo motar asibiti aka shimfida wani katako aka ce mu zauna, kowa na magana damu nesa da nesa.
Aka kawo mu FMC da za a bude mu fito aka rika fesa mana wani maganin feshi ana mana tsawa kar mu taba komai, aka shigar damu wani daki muka iske mutane uku a ciki.
Abin takaicin, kyama da rashin magana mai dadi da ake nuna mana shi ne bacin rai, abu na biyu mun baro iyalan mu da muke kula dasu amma wai sai aka sai masu abinci na naira dubu talatin da biyu aka aika masu, masara gyero, da sukari.
Don kyama da farko, in za a kawo mana abinci sai a buda dakin a turo mana kamar dabbobi, muka shaida masu cewa in aka sake haka, duk wanda ya kawo zamu bishi da gudu mu kama shi mu rike sai kowa ya shafe shi cikin mu, duk abin da ake zargin mu, mu goga wa mutum ya zama namu.
Yace tun da aka kawo mu, ba wanda yayi wani kwanciyar rashin lafiya amma an ce bamu da lafiya.
Malam A yayi ikirarin ba wanda aka gwada duk gidan su sai shi, duk da ya dau kwanaki yana mu’amala da mutane, kuma tun da ya baro ba wanda aka shaida masa koda atishawa yana yi.
Wani daga cikin su da zan kira da Malam B Dan shekaru 25.yace shi sana’ar aski yake yaji mura ta dame shi, da kanshi ya je asibitin FMC yana zuwa aka haska mashi fitilar gwada zafin jiki, sai kawai aka rike ni aka ce in kwanta za a gwada ni aka debi samful aka dawo aka ce nima ina da Coronavirus, aka je aka rufe shago na akwa je gidanmu ana dibar samful din kowa.
Malam B yace, bayan nazo murar ta sake ni garau nake jin kaina, in banda takurar zama waje daya amma wai duk da haka bani lafiya.
Wani aboki na aka zuga shi, ya kai kanshi yanzu haka yana can tsare a wani dakin. Yace sai da na gargade shi, nace wane ka tada hannunka yaki ji, yanzu anyi ram da shi.
Malam C dan shekaru 23.yace Abuja yake aiki yana jin za a rufe ya dawo gida kwanan sa 25 da dawo wa, sai yaji masassara mai tsanani naje aka gwada ni aka ce typhoid ce, ina shan magani naji bata tsaya ba na sake komawa asibiti sai aka ce za ai mani gwajin Coronavirus naje a gwada, bayan kwana uku aka kira ni ina zuwa aka yi ram dani, aka je gidanmu aka debi gwajin mutane, aka je akayi feshi a gidan yanzu ina nan ko ciwon kai babu, amma wai banda lafiya ina da Coronavirus.
Dukkanin su sun tabbatar mana ana ciyar dasu a inda suke, sun ce magunguna kala uku kawai ake basu, sai Kuma gwada jininsu da zafi da ake yi.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta da ke bisa yanar gizo.www.taskarlabarai.com tana a duk shafukan sada zumunta. Tana da ‘yar uwa da Turanci mai suna The links News. dake www.thelinksnews.com. duk Kira ga 080 88895277 WhatsApp 07043777779