YADDA ALLAH YA TSARE NI DAGA SHARRI

0

YADDA ALLAH YA TSARE NI DAGA SHARRI

Daga Danjuma​ Katsina.

Alhamdulillahi khasiran na tsallake wannan makidar.shekaran jiya nayi wani rubutu Mai taken Bani nayi fassarar ba.kuma rubutun ya yadu kamar wutar Dani.jaridu biyu sun buga rubutun.. leadership Hausa da Al. MIZAN
ABin da ya faru .shine talata wani ya Kira ni.da asuba in lazumi.yace wani algungumi ya fadawa gwamna wai Ni na fassara rubutun..nayi dariya ..nace Allah shine ubangiji na.
Da safe na Kira Abdu Labaran SSA press.. nace ina son ganin gwamna yace inzo.nayi niyyar. Kawai in hadu da gwamnan in yayi man maganar in Masa .in bai Mani ba in Masa wata maganar..
Ban fada ma Labaran komai ba.
Na samu ganin gwamna da karfe 11 50.mu uku a ofis din .Ni Labaran Abdu sai kwamishinar lafiya..ba wani chanji tare dashi a kaina.nayi masa maganar da Zan Masa muka fito.bai Mani waccar maganar ba..banyi Masa ita ba.
Bayan mun fito..wajen karfe 1.30pm na yamma wancan ya sake Kira na.yace .. lallai algungumin can fa ya dage .sai a dau mataki akan ka..na fada masa cewa .ai har wajen gwamnan naje kuma bai Mani maganar ba..yace bai isa ba..nace Masa bani tsoron komai zai biyo da akan laifin da nayi ne..Amma tun da sharri ne ! Zan yaki abin..
Nan da nan sai na fara bugawa wasu waya ina shaida masu abin dake faruwa…da yamma kuma na rubuta sakon can da na yada shi…
A halin Dan Adam .akwai Wanda nake zargi( bani da tabbas ) Don Mai Mani wayar bai fada Mani ba…ko waye..Wanda ke Mani wayar ban ma sanshi ba…Amma dai yace kaunata ya sa yake fada Mani sakon..
Na tashi karfe Daya na dare..nayi rubutu har kalma dubu da Daya (1001)akan wancan da nake zargi…na Gama rubutun, biyar na asubar larabar data gabata 12/9/2018
Na bi rubutun na tace ..da safe na rika buga waya ina Kara tabbatar da abinda na rubuta.
Da safe karfe goma na ranar laraba .wani ya sake Mani waya yace…anyi Mana jawabi Akan ka ..amma ba a ce mu dau wani mataki ba..yanzu umurni muke jira.don Haka in akwai yadda zaka gyara matsalar dake neman tasowa ka gyara.kafin umurni yazo.
Muna Gama magana na Kira lauya.shugaban Dangana. Chambers nayi masa bayanin duk abin dake faruwa.kuma na fada masa duk abin da ya biyo baya ga abin da. Nake so.
Nan da nan na tura rubutun da nayi ga editocin da suka buga fassarar can na kuma nemi cewa su buga Don su wanke Ni daga zargin​ fassarar da Ban San da ita ba..
Dayan editan yayi dariya yace..wani ne dai ke nemanka da sharri.amma ai da su tambaye mu..yace sashen fassara na jaridar su sukayi aikin fassarar..yace in da wani Abu ya same ka Akan wannan fassarar da Shafi Daya zamu buga tallar cewa ba ruwanka.
Na tura wa .wani Dan uwana wancan rubutun .nace da zarar .yaji labari iri kaza .to ya sake shi..na tura Masa lambobin da emails emails da zai tura rubutun…su kuma duk wadanda za a tura. Mawa na Kira su.mukayi bayani dasu.
Editocin wadannan jaridun guda biyu ..wadanda ake zargin nayi fassarar na tura masu.duk sun buga a jaridun su..na yau Alhamis…cewa ba ruwa na..(ga kwafis din jaridun a Hannu na)
Ina Jin wannan makircin Allah Mai tausan Wanda ake son a dau Alhakinsa.ya kare shi..
Amma har yanzu tsugunne Bata kare ba( Wanda nake zargi ) in ta tabbata shine..Zan saki rubutun da nayi akansa.. duniya ta San waye shi.nayi rubutun da Hausa da turaci.na turancin Yana da taken THE UNATHOURIZED BIOGRAPHY.OF ……na hausar kuma shine WANE NE……..
Dukkaninsu na saka suna na da adireshi da lambar waya da ta email..editocin da zasu buga ..Ni Zan buga masu waya. In tabbatar masu rubutu na ne. Zan kuma aika masu da ofishiyal email​ di na.
In na samu tabbacin Wanda na ke zargi shine ..Zan saki rubutun a kansa ..sai dai yayi karshen abinda yake Jin zai iya a kaina..na shirya Masa..
Na gode da addu ar da nasha. Danjuma kt

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here