YADDA KIDNAFAS KE TSARA SHIRINSU DAGA MANYAN GARURUWAN KATSINA 

0

BINCIKEN MUSAMMAN
YADDA KIDNAFAS KE TSARA SHIRINSU DAGA MANYAN GARURUWAN KATSINA

A shekarar 2018 jaridar *TASKAR LABARAI*, ta fitar da wani gargadi a kan yadda bunkasa da salon da barayin daji masu dauke da makamai ke sake lale.

Gargadin sun shelanta shi ne a tsarin sanarwa ga manema labarai, mai taken: ‘A yi gaggawar daukar mataki kafin lamarin ya wuce iyaka.’

Rubutun, wanda jaridu da yawa a kasar nan suka yi amfani da shi, kuma har yanzu haka yana a kan Yanar Gizo ga duk mai bukata.

A rubutun sun jawo hankalin jami’an tsaro da hukumomin kasar nan cewa, abin da ke faruwa zai kara muni in ba a dau matakai a cikin gaggawa ba. Sun kuma ba da karin haske a kan abin da suka gano.

*TASKAR LABARAI* da sauran jaridun *KATSINA CITY NEWS* da *THE LINKS NEWS* sun yi wani bincike na musamman a kan ko wadannan miyagun sun canza salo, kuma suna sake lale!

Abin da muka gano yana da tada hankali da kuma ba da tsoro. Akwai kuma bukatar a farga tun kafin lamarin ya kara muni ya wuce iyaka. Ya zama ba wanda ke da tabbas a kan sa, in yana da rufin asiri ko yana da dan’uwa mai mulki ko abin hannunsa ko abokai.

Bincikenmu ya tabbatar mana da yawa daga cikin wadannan miyagu suna bude wuraren kasuwanci a manyan garuruwa, kuma suna ba wadansu da za su kular masu da kasuwanci nasu.

Bincikenmu ya gano yanzu suna da tsari na zamantar da mugun aikin nasu, inda suke samar da matasa a garuruwa wadanda za su rika ba su labarin wa ya kamata su dauka su samu kudi?
Su wadannan gungu aikinsu shi ne nemo wanda ya kamata a dauka da samo bayani a kan sa, ko dai yana da kudi, ko ya samo kudi, ko yana da wadanda za su iya ba da kudi.

Wadannan aikinsu su kuma tattaro bayani a kan wanda za a dauka, karfe nawa yake barin gida da ina da ina yake zuwa? Su waye abokansa?

Suna shiga kafofin sada zumunta irin su Facebook su ga yadda yake bayanin zirga-zirgar sa da tasirinsa a cikin al’umma. Idan wadannan suka gama aikinsu, za su ba gungu na gaba, kamar yadda bincikenmu ya gano mana.

Su wadannan gungun sune masu daukar nauyin masu nemo bayani, idan suka amshi rahoton sai su yi nazarinsa, in sun gamsu sai su tura wa wadanda ke daji da bayanin wadanda za a dauka.

Su kuma na daji, za su nemi sa’a a wajen Malamai da Bokayensu, sai su fitar da ranar da za su je.

Daga nan za su fitar da rana, sai su sanar da masu daukar nauyin aikin. Su kuma za su bincika su ga ta yi daidai da yanayin yadda wanda ake son dauka ke zirga-zirgar sa? In ta yi sai su tura masu Direba da mota a inda aka yi mahada, sai ya dauko wadanda za su yi mummunan aikin daga daji.

In Direban ya dauko su zai kawo su cikin gari su hade da wadanda suka kawo bayani a kan wanda za a dauka, shi ne zai masu jagora har zuwa inda za su yi abin da ya kawo su.

Ana daukar mutum, Direba zai sake daukar su dama dan gari ne, ya san hanyoyin garin kamar bayan hannunsa, zai fita da su sai zuwa daji ya ajiye su, ya komo gari.

Daga nan masu daukar nauyi da masu ba da labari da tattara bayanai za su tare kusa da wanda aka dauka suna daukar labarai da jin me ake shiryawa, da bin kafofin sada zumunta suna jin tattaunawar da aka yi a kan wanda aka dauka, sannan su kuma sanar da mutanen da ke cikin daji duk abin da ke gudana.

Masu aikin tattaro labaran za su rika bin shafukan Yanar Gizo suna jin me ake fadi? Suna sanar da wadanda ke a daji.

Masu daukar nauyi za su rika sunsunar labari a cikin jami’an tsaro su ji ko an sanar da su, ko ana wani kokarin kwato wanda aka kama da karfi.
Kowane bangare zai rika aikinsa don ya tabbatar da an yi nasarar toshe duk wata kafa da asirinsu zai tonu, saboda sun san in asirinsu duk kashinsu ya bushe.

In aka biya kudi, rabawa ake daidai yadda aka tsara aka amince kafin ai aikin. Direba za a ba shi nasa kason wadanda suka kawo labari a ba su nasu, wadanda suka dau nauyi a ba su nasu, masu tsaron wanda aka dauko da kuma masu bindiga kowa a ba shi nasa.

See also  AN SACE FIRINSIPAL A BATSARI

Binciken ya gano ana shigar da mutane su zama bangaren wannan gungu ne ta hanyoyi daban-daban. Wasu ana kwadaita masu akwai riba a ciki in aka yi na farko da su sun shiga ke nan ba fita, in suka yi kokarin fita za a yi masu barazanar tona masu asiri ko kisa.

Wasu kuma suna shiga ne ta hanyar in an kama su an sako su, sai a ce in suna son mai da kudinsu, to su nuna wa za a dauko, da sun amince suka fara sau daya shi ke nan ba fita.

Wasu kuma barazana ake masu; “Ka ba mu hadin kai, ko za mu zo mu tafi da kai har inda kake.” Da mutum ya fada tarkon barazanar shi ke nan babu fita.

Wasu kuma yaran masu gida ne da ake jan hankalinsu su ci amanar maigidansu ta hanyar ba da bayanai da sanya ido da ma zirga-zirgarsa

Su ma ana yaudare su da sanya masu zuma a baki. Da sun aikata sau daya, sun shiga gorar da babu fafi.

Bincikenmu ya gano cewa a kowane tarko so ake ka shiga sau daya, daga nan ka zama nama, kuma ka shiga ke nan ba fita. Duk wani yunkurin fita, za ka yi ta ranka ne, ko a cinna maka jami’an tsaro.

Bincike ya tabbatar wannan gungun suna kara yawa a manyan burane, kuma kusan duk ta’asar da ake aikatawa a garuruwa da hannun irin wadannan tsararrun gungun tsundum dumu-dumu.

Binciken ya gano mana, wadannan suna tsara kansu a tsanake, kuma yanzu sun fara yawa a garuruwan Katsina, Funtua, Daura da sauran wasu manyan garuruwa da hedkwatar Kananan Hukumomi.

Mun gano ba su haduwa fuska da fuska sosai, mafi yawan tattaunawar ta waya ake yi da kalmomin da sune suka san ma’anar sakon. Misali; ‘ina da gida na sayarwa, kuma za a ci riba sosai’. ‘An gama komai?’ Kwarai kuwa’. ‘Nawa ne la’ ada?’ Da irin wadannan boyayyun bayanai suke magana da junansu.

Mun gano wasu zaman daji ya fara isar su, don haka sukan shigo gari su huta, amma yadda suke yi shi ne, na Kaduna sai su zo Katsina inda ba wanda ya san su. Na Katsina sai su je wajen Kano ko Kaduna.

Ya suke sace mutum? Har yanzu tsarinsu daya ne, shi ne su tabbatar da an dauki mutum ba tare da an kama su ba, don haka suna duba dare, ko mutum ya kasance inda babu kowa. Suna fatan su ga titi fayau ba jami’an tsaro masu bincike.

Mun gano in za su fito aiki irin nasu masu bindiga sukan sha wasu kwayoyi da hade-hade da zai cire masu duk tsoro, amma Direba da wani za su zama cikin hayyacinsu ko da ta-baci su fitar da su.

Mun gano wasu sace-sacen mutane da aka yi misali a Katsina, Kankia, Funtua da Musawa, duk akwai alamar irin wannan tsararren aikin da muka fada a sama.

Tun wuri ya kamata a fara daukar matakan da suka dace don shawo kan matsalar tun kafin lamarin ya kai inda ba a tsammani.

Babban matakin da ya kamata a dauka shi ne kowa ya shiga cikin taitayinsa da kuma taka-tsantsan, sannan sai jami’an tsaro su kara kokari.

Mun hada wannan rahoton ne ta hira da wasu da aka sako bayan an dauke su da tattaunawa da wasu masu aikata laifin da aka kama yanzu suna hannun jami’an tsaro da wasu da suka yi ikirarin an taba tuntubarsu su shiga cikin gungun don a samu kudi.wasu kuma tsaffin barayin daji ne da sukayi ikirarin sun tuba.

Gobe litinin jaridun katsina city news da the links zasu saki wannan rahoton da harshen turanci.

Hotunan wadansu da ake zargin masu ba bandit labarai ne ? Da sojan sahel SANITY suka kama ,suka kuma gabatar da su ga manema labarai. A faskari ta jahar katsina.

An kama shi bayan zargin ya amshi kason shi daga wajen kidnafas

 

Binciken hadin gwaiwar jaridar *TASKAR LABARAI* da *THE LINKS NEWS* da *KATSINA CITY NEWS* da suke a kan www.thelinksnews.com. da www.taskarlabarai.com da www.katsinacitynews.com. duk sako a aiko ga 07043777779. 070 88885277.Kira Email. Katsinaoffice@yahoo.com. newslinks@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here