YADDA KWANKWASO YA BI UMURNIN JONATHAN!

0

YADDA KWANKWASO YA BI UMURNIN JONATHAN!

Daga Ahmad

Wani bincike da Jaridar Taskar labarai tayi a kan yadda duk da jin Kai na Kwankwaso, ya iya kaskantar da kansa yaje har gida ya samu Malam Ibrahim shekarau, don su daidaita tun da ya dawo jam’iyya daya da Shekarauvdij wato PDP.

Binciken mu ya gano ba haka kawai siddan ruwa da Da tsaki ba ya kai kansa ga Shekarau. Majiyarmu ta tabbatar mana tun lokacin da Kwankwaso ya so koma wa PDP ya nemi ganawa da Jonathan wanda yake shi ne uban jam’iyyar PDP, amma Jonathan yaki ganin sa yace sam ba za su amshe shi ba sai da amincewa da kuma sasantawarsu da shekarau.

Majiyarmu tace kwankwaso yaso ya gana da wasu jiga jigan PDP na kasa duk suka kife masa ciki suka ce sai ya fara ganawa da Shekarau, kafin su ganshi.

Ance ganin cewa ba yadda ya iya dole ya fara neman sasantawarsu da shekarau shi ne zamansa lafiya indai yana son komawa PDP
akan haka yabi wasu hanyoyi.

Ance da farko shekarau yaki amincewa da ya gana dashi, amma aka yi ta bashi magana majiyarmu tace, kin sakin jiki da dawowar kwankwaso PDP ya sanya da aka shelanta a gaban zauren majalisa cewa, ya koma
sai shekarau ta hannun mai taimaka masa a hudda da manema labarai, Sule Ya’u Sule ya fitar da wata takarda wadda a ciki Shekarau ke cewa, yana fatan dawowar kwankwaso PDP zai zama mai biyayya ga kundin tsarin mulkin jam’iyya da tsarin da PDP kan bi a tafiyar da gudanarwarta, yace suna fata Kwankwason da suka sani yanzu ya canza, ba na da can bane.

See also  AYAR ALLAH A KOFAR DURBI KATSINA

Majiyarmu ta tabbatar mana ban magana ta sanya Shekarau ya gana da Kwankwaso wanda shi ne sharadin da jagoran jam’iyyar PDP tsohon shugaban kasa Jonathan ya dorawa Kwankwaso, suna wannan ganawar sai shi ma shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya amince ya gana da shi kwana daya bayan haduwarsu da Kwankwaso.

Yanzu kuma an saka wata rana ta ganawarsu da Jonathan, wadda ita ce babban gurinsa.

A wannan sabon babin siyasa da ya Shiga
majiyarmu tace an shirya biki gagarumi don kawata wannan rana wadda ake dakon zuwanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here