YADDA MAHARA SUKA TARE GALADIMAN KATSINA

0

YADDA MAHARA SUKA TARE GALADIMAN KATSINA
Daga Taskar labarai
A ranar litinin 7/1/2019 wasu mahara dauke da makamai suka tare motar galadiman Katsina.. hakimin Malumfashi ..ta jahar Katsina..Dr Mamman Nasir tsohon babban alkalin kotun dauka ka Kara ta Najeriya.
Kamar yadda binciken Taskar labarai ya gano .. Galadima ya baro Katsina Inda ya je ya kwana daya.yana kan hanyarsa ta komawa Malumfashi..wajen Bayan kammala sallar Isha i, dai dai wani. gari Mai suna gora .kusa da Yar mama.
Sai wadannan mahara suka tsaida su, ance kafin su .sun tsaida wasu motocin .har sun rike da wata Mata.suna Shirin tafiya da ita. Sai ga motar galadima ta iso wajen
A cikin motar . Galadima na baya.zaune, a gaba direba da P.a na galadima suna zaune.
Maharan, suka ce direban ya fito.yana fitowa shi da p.a .sai suka leka motar suka ga galadima ..sai Daya cikin maharan yace yau ba .sa.a .maigida muka tare.
Sai maharan suka tambayi diraban kudi.ya kawo Dan abin dake wajen sa ya Basu..suka ce ya bude motar ..direban tsoron kar ya bude su taba lafiyar galadima sai yaki budewa.
Wannan ne, har ya kawo Yar gardama a tsakanin su.har Daya na cewa ..in kaki budewa zamu harbe ka.daga baya ya bude motar ,suka duba but na motar da gaban wajen direba suna neman kudi ko wani Abu Mai amfani..
Daga Nan. Sai suka ce, direban ya jira a. Mota .sai sukace ..p.a na galadima Wanda suke tare ..Mai suna sani.ya bisu su .ya gaida ogansu. Ana cikin Haka sai ga Yan sanda sun iso.nan suna isowa aka fara musayar wuta da bindigogi.
Duk abin Nan da ake . Galadima na cikin mota zaune ..kuma hankalinsa kwance a tsanake ba tare da wani firgici ba.sai ma latsa wayarsa yake.
Dama maharan suka leko suka gaishe shi, sai daka masu tsawa ya kuma gargade su, da suyi maza su bar hanyar Nan ..in kuma ba Haka ba, zasu mutu..sai Daya ya Rika cewa ayi hakuri yallabai…kamar yadda majiyarmu ta shaida Mana.
Koda Yan sanda suka zo ..sai direban ya tuko motar zuwa karasowa Garin malumfashi.maharan sun tafi da p.a da galadima Mai suna Sani.amma galadima da direbansa .suna Malumfashi..cikin koshin lafiya.jama a na zuwa yi masu jaje.
_________________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake da cikakkiyar rijista dake Bisa Yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta..na Facebook, Twitter’s​ instigram,da you tube…da whazzapp a lamba 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here