YADDA MUKA MOTSA KATSINA DA KANO AKAN RASHIN LAFIYAR MARIGAYI UMARU MUSA YAR’ADUA.
Daga Danjuma Katsina
Lokacin da marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar ‘adua baya da lafiya, kasar nan ta dau zafi inda kudu da yamma suka hada kai akan Umaru ya ajiye mulki, arewa kuma aka yi shiru sai masu goyon bayan kudu ke magana.
Kafofin watsa labarai sun ruwaito wani babban mutum daga Katsina yana cewa shima yana goyon bayan wancar kira na ‘yan kudu. Sai kawai naga kalamin mutumin can bai dace ba, amma na dauka kila an masa kage ne.
Sai na ga wasu a arewa sun yi kira cewa ya janye zancensa ko ya karyata in har bashi ya fada ba. amma akayi kwanaki, bai yi ko daya ba.
Kishin Katsina da tausayi ga Umaru akan halin da yake ciki sai ya taso mani don haka, na tsara jerin gwano da taron manema labarai wanda duniya za ta san cewa a gida Katsina ana tare da Umaru.
Na tsara, a rubuce,amma ba kudin aiwatarwa. sai na nufi gwamnatin jiha, duk wanda nayi wa magana, sai ya gwalashe ni, in auna wannan in saka wancan.
Sai na nufi wajen Alhaji Zubairu Ali Gafai, na fada masa abin da ya kamata ayi, nace yana da wanda zai dau nauyi shi kuma ya jagoranci shirin?
Zubairu Ali yace akwai, shi ne Muttaqa Rabe Darma, nan take ya shiga wani daki ya kira shi, ni kuma ina zaune a falo, can ya fito yace ya amince.
Nan na ba Zubairu tsarin duk abin da za ayi da yadda za ayi, a rubuce.aikin ya hada da jerin gwano zuwa gidan sarki da kewayawa cikin gari da taron manema labarai.
Muttaqa ya dau nauyi, tunani na ne Zubairu ya aiwatar, a ranar da za ai bayan na tabbatar da komai na tafiya dai dai, na bar katsina na nufi Kano. Abin da akayi yayi tasirin gaske.
Akan hanya, ina yada zango ina waya, don jin labarin yadda komai ke gudana. Na tafi Kano don a Kano ma wani Dan Kano( shima yanzu wani jigo ne a kasa) dake goyon bayan Umaru ya bamu aikin shirya irin jerin gwanon Katsina na goyon baya.
Kano a lokacin jam’ iyyar adawa ke mulki bata tare da gwamnatin tarayya na iske a Kano ‘yan sanda sun hana taron na iske masu shirya shi har sun janye duk wani shiri nasu.saboda da tsoro da rashin sanin ta inda za su fara.
Shi kuma wancan babban na Abuja sai waya muke, yana me ke faruwa? Ina isa na hadu da abokan aiki sun karaya suna neman a janye, nace a a ba za a janye ba, sai dai a canza yadda za a yi.
Kudin aiki suna a wajena nace a samo mani mutane hamsin yan ta kife,daga unguwannin Kano daban,suna zuwa na basu horo na gaggawa.da abin da zasu yi na wani jerin gwano a wurare uku cikin Kano suna daga hotunan shugaban kasa da goyon bayan shi yadda zai jawo hankalin kowa, suna Rabar da takardun goyon bayan shi, a cikin rumtsin su bace cikin mutane mu sake haduwa a inda aka tsara.
( wata Rana zan rubuta ya mukayi )
Sun aiwatar a lokaci guda, Kafin kace meh labarin ya watsu garin ya dau zafi, ba wanda yaga wadanda suka yi amma ga Dubban takardun da suka Raba, dole ya zama labari a kafafen watsa labarai.
Duk mun hadu ba wanda aka kama ba wanda yaci amanarmu, ya tona a kama mu. Na sallami kowa na kamo hanyar dawowa a Katsina. Ina tafiya ina sauraren redio ina jin yadda lamarin ya zama abin tattaunawa.
Salon da nayi amfani dashi a karatun gwagwarmaya muna kiran shi da Hausa. SAWU A SAHARA( footprints in desert)yanzu Idan mutum na tafiya cikin yashin Sahara, ga iska in ya taka ya dage kafar cikin mintuna za a sake ganin sawun? Haka ake son kaje wuri kai aiki, ka isar da sako, kuma ka fito lafiya.
A Katsina matata ta kan gane, in ina cikin wata harkalla ko ana shirya ta dani, tun da tasan a dabi’ance bana fada mata. Sai kaji tace, “aji tsoron Allah” ni kuma sai ince , mu ‘yan gwagwarmaya ne, ba masu aikata laifi ba.
Ranar ma ina isowa gidan wajen daya na dare, sai tace ga alama baka garin nan, nace eh Naje Kaduna ne, shi yassa nayi dare, bata yarda ba amma tasan amsar da zata iya samu kenan. Sai ta maimaita abin da ta saba fada, ni ma na maimaita mata nawa.
Danjuma shi ne mawallafin jaridun The Links News da jaridar Taskar Labarai.