Yajin aikin masu mashina: Motocin Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano

0

Yajin aikin masu mashina: Motocin Kurkura sun maye gurbin adai-daita sahu a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Tun da safiyar yau ne dai aka wayi gari da yajin aikin masu Adai-daita sahu a jihar Kano inda ya tilastawa mutane da yawa hawa akori kura da domin fita wuraren kasuwanci da ayyukansu na yau da kullum,

A zagayen da wakilinmu na Kano ya gudanar ta gano yadda mutane ke rigegeniya wajen hawa a kori kura a wurare da dama ko kuma su rasa abin hawa.

Manyan hanyoyin da aka gano masu hawa akori kurar na rububi sun hadar da Dan dinshe zuwa Kwari da sabon titin Mandawari zuwa Kwari da Kurna zuwa Ibrahim Taiwo da kuma titin Panshekara zuwa Kofar Fanfo da tituna da dama a cikin birnin Kano.

See also  Buhari ya baiwa jami'in dan sanda wanda ya ki karbar cin hancin $200,000

Su kansu masu kurkurar jamaa sun koka akan yadda su yan kurkurar suka ninka kudin hawan, inda suka ce ko a adaidaita inda suke biyan 100 amma yanzu a Kurkura 300 suke karba.

Masu Adaidaita Sahu a kano dai sun fara yajin aiki ne tun bayan da gwamntin Kano ta ce sai sun bayar da harajin shekararar da ta gabata da kuma na kullum naira Dari dari.

A halin da ake ciki dai yanzu a Kano duk inda ka duba jamaa ne zaka gani suna tafiya a gifen titinu zan zuwa wajen harkokinsu nau da kullum, inda masana ke cigaba da nuna damuwarsu a kan wannan yajin aiki na masu adaidaita sahu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here