’YAN BINDIGA SUN KAI HARI JIBIA A JIHAR KATSINA
……Ana hada masu kudi don….
Abdullahi salihu jibia
@ jaridar taskar labarai
Mahara sun kashe mutane biyu yayin harin da suka kai mazabar Mazanya da ke cikin Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina da misalin karfe 10:30nd.a ranar Alhamis da ta wuce
Mutanen da suka harba sun hada da Bilyaminu Haruna da ke sana’ar tuka babbar motar a gidan Alhaji Aliko Dangote da kuma Isihu Yunusa, wanda shi kuma mahauci ne da ke sa’anar sai da nama.
Wasu maganau sun shaida wa jaridun nan cewa, maharan suna zuwa garin kai tsaye sun yi tsinke ne gidan wani hamshakin Attijiri da ake kira Alhaji Abdullahi, sai dai sun yi rashin sa’ar tarar da shi.
Haushin rashin samun Alhaji Abdullahi a gida ya sa ’yan bindigar sun huce fushinsu a kan mutane gari, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Sai dai duk wannan kisan da suka yi, maharan sun bukaci jama’ar wannan yankin da suka kunshi garuruwa masu yawa su biya wasu kudade in suna so a yi sulhu su daina kai masu hare-hare.
Tuni har jama’ar garin Mazanya sun kai wa Limamin garin nasu Naira dubu 30, yayin da jama’ar garin Magaji za su biya Naira dubu 70, su kuma Kwarare za su biya Naira dubu 150. Tuni dai har sun tara Naira dubu 500.
Yanzu haka dai garin Magaji ya zama kufai, jama’a sun watse saboda yadda ’yan bindigar suka addabi jama’ar yankin nasu.
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 081 377777245