YAN BINDIGA SUN KAI HARI WANI KAUYEN BATSARI.

0

YAN BINDIGA SUN KAI HARI WANI KAUYEN BATSARI.
Daga wakilan taskar labarai

A ranar alhamis 05/03/2020 da misalin 12:30am na dare, wasu gungun ‘yan bindiga suka farma wani kauye mai suna Babbar Santa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, sun yi harbe-harbe kamar yadda suka saba.

Sannan suka yi awon gaba da garaken tumaki da shanu ba tare da samu wata tirjiya ba. Amma da farko mazauna yankunan sun yi kokarin tunkarar su, amma sai suka ga abun yafi karfin su.

Don haka, ne suka dangana suka bari ga Allah. Lokacin da suke tafiya da dabbobin, ‘yan bindigar sun yi ta kururuwa suna a taimaka, lokaci guda kuma suna antayar da ruwan harsashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here