YAN BINDIGA SUN SAKO ALKALI HUSAINI ISMAIL

0

YAN BINDIGA SUN SAKO ALKALI HUSAINI ISMAIL
@ katsina city news
Jiya jumma a 10/7/2021 yan bindiga suka sako Alkali husaini Ismail wanda suka dauke a harabar wata kotu a karamar hukumar safana kwanaki hamsin da hudu da suka gabata.
Yan bindigar sai da suka amshi naira milyan daya sannan suka sake shi a wani gari mai suna muniya dake iyaka da safana da batsari.
Tun da aka dauke shi.wasu biyan Allah suka sadaukar wajen tsayama Iyalin da kuma neman taimako wajen jama a don hada abin da za sako shi.
Wadannan bayin Allah sune Hasan da husaini yar adua wadanda suke da shafin labarai da yada addinnin musulunci da ake kira HK tv online.
Wadanda suka dauke shi da farko sun ce a basu naira milyan hamsin da akayi ta magana suka kuma samu tabbacin ba kudin.sai suka dawo milyan uku.shima suka lura ana bara a ranar laraba 7/7/2021 sai suka amince da milyan dayan da aka tabbatar masu ita kadai aka tara.
Wani bawan Allah dan asalin batsari da hassan yar adua suka je har bakin dajin .inda aka samu wani mai mashin amintacce da ya kai masu a tsakiyar dajin da suke a same su, yankin wani gari mai suna muniya cikin safana iyaka da wagini.
A daren jiya suka sako shi.yana fitowa bai San koina sai ya nufi gidan garin da ya fara isa.
Daga nan ne alkalin yayi ma yan uwansa alkalai waya , suka dauko mota suka kawo shi katsina.
Hoton alkali husaini Ismail dake wannan labarin an dauke shine bayan anyi masa aski daga fitowar sa a daji .

See also  ABIN DA KE DAMUNMU YAFI ANNOBAR CORONAVIRUS


Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.081377777245
Katsinaoffice@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here