“YAN BINDIGA SUN ZAMA SARAKUNA A YANKIN BATSARI 

0

….Suna gayyatar ai masu noma

….sun sace wani jami in tsaro

….suna tare hanya da Rana tsaka

Misbahu A.Batsari

@ katsina city news

Hare-haren ‘yan bindiga masu satar shanu, garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, na neman gagarar Kwandila a yankin Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

 

Wani abun mamaki kuma shi ne, yadda ‘yan bindigar suke neman dawo da bautar da mutane ta fuskar tilasta masu yin noma a gonakansu.

 

Domin kuwa ko a ranar Asabar da ta gabata sai da suka raba wa mutanen kauyukan yammacin Batsari goron gayyata, su je su yi masu noma. Kuma duk sun amsa, domin gudun abun da zai biyo baya.

 

Ko a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan bindigar sun kama wani mutum daya a gonarsa da ke Yasore, inda suke tuhumarsa da laifin kin zuwa noma da suka gayyace shi. Amma sun kyale sauran abokan aikinsa saboda su sun je aikin gayyar da suka gayyace su.

 

Yanzu haka sun bukaci kudin fansa Naira miliyan hudu kafin su sake shi.

See also  Jam'iyyar PDP A Jahar Katsina Ta Yi Tir Da Allah Wadai Da Kisan Mutane 41 a Yargoje

 

A wani labarin kuma, wasu mahara sun shigo cikin Batsari da daren ranar Litanin 25-07-2022, inda suka yi awon gaba da wani jami’in dan sanda, Malam Sule a lokacin da yake kokarin shiga gidansa da ke Unguwar Leko da ke cikin garin Batsari.

 

Haka ma a kauyen Yasore, wasu matasa su shida sun je noman yammaci, sai ‘yan bindiga suka cafke su, amma sai suka sako mutum banyan sun caje shi sun samu Naira dubu 20. Sai suka ce ya fanshi kansa, amma ya je gida ya karbo masu Naira dubu dari, N100 na sauran mutum biyar din, in ba haka ba za su harbe su, domin ba tafiya za su yi da su ba.

 

Daga bisani aka hada kudin aka kai masu, suka sake su.

 

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@www.taskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

070 43777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here