‘YAN KWANKWASIYYA SUN GURFANAR DA GWAMNA GANDUJE GABAN KOTU
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kungiyar Ɗariƙar Kwankwasiyya reshen jihar Kano ta maka gwamnatin jihar Kano gaban kuliya don hana ta ciyo bashin €684,100.100.00 daga China Development Bank don samar kuɗaɗen gudanar da aikin titin jirgin ƙasa a jihar.
Kwankwasiyya ta kuma rubuta ƙorafi a kan gwamnatin jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar Kano zuwa Shugaban Majalisar Dattijai ta Najeriya, Ma’aikatar Kuɗi ta Ƙasa, Ofishin Bada Bashi na Ƙasa, Ofishin Jakadancin China da Chinese Development Bank, tana mai cewa an saɓa ƙa’ida a buƙatar ciyo bashin, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito a shafinta,
A wata sanarwa da ɗan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na 2019 Comrd. Aminu Abdusalam ya sanya wa hannu, ya ce Kwankwasiyya ta yi kira ga kowa da kowa da ya ƙalubalanci wannan shiri na ciyo bashi, saboda a cewarta kuɗin zai ƙare ne“a aljihun babbar rigar Gwamnan Kano”.