YAN MAJALISUN TARAYYA DAGA JAHAR KATSINA..BASU YI WATA HOBBASA BA

0

YAN MAJALISUN TARAYYA DAGA JAHAR KATSINA..BASU YI WATA HOBBASA BA…..INJI SANATA IBRAHIM IDAH
Daga wakilan mu
Wata Hira da gidan talabijin na NTA Hausa yayi da tsohon sanatan Katsina ta tsakiya..Alhaji ibrahim idah..ya bayyana cewa wakilan dake majalisun tarayya dake Abuja daga Katsina Basu yin wani abun azo a gani na kare Martabar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ..Sanata idah yace in ma suna yi, Ni ban gani ba..ko kuma ince ban gamsu ba.
Ibrahim idah Yana maganar. Ne a shirin na NTA Hausa Mai suna Turmin danya. Wanda Umar Muhammadu Karachi ke gabatarwa.kuma aka watsa shi Alhamis 13/9/2018.da karfe takwas zuwa Tara na safe.
Jaridar Taskar labarai ta kalli Shirin kaf dinshi..Inda Ibrahim idah ke cewa ya sake fitowa takara ne .saboda tun da ya bar Sanata yankin mazabar sa..ake ta ci baya..komai na neman tsayawa cak. Yace cigaban da suka kawo lokacin da suke kan kujerar yanzu ..Sam abin ba Haka yake ba.
Yace hatta wadanda ke a majalisar tarayya daga Katsina basa yin abin azo a gani na kare Martabar shugaban kasa..sanatan yace i””na Sanata marigayi umaru Musa yake shugaban kasa kuma ya fara Rashin lafiya..mune muka tsaya kar a ci masa mutumci.muka dage a majalisar ta kasa…ya tambayi Mai gabatarwar yanzu Yan majalisar mu daga Katsina me suke yi.?

See also  ‘Yan sanda a Katsina sun yi artabu da ‘yan ta’adda

Sanatan ya Kara da cewa majalisar kasa ,waje ne .na gogaggu ,wayayyu, masu ilmi wuri ne, na ba Sani ba. Sabo .wuri ne na duniyar annabi shaho kowa ya yagi rabonsa
Yace a irin wannan wuri in ka yi kuskuren..tura wanda bai dace ba..to kayi kuskuren da baya gyaruwa sai Bayan shekaru hudu..
Sanatan yace .ya Kamata jama a su San wa zasu zaba su tura a wajen!..ya Kara da cewa shi Ibrahim idah na da duk Yana
da abin da ake nema kuma in aka tura shi ba zai bada kunya ba.
Sanatan ya yi Kira da a abar suka ko kushen shugabanni yin Hakan bai dace ba kuma ba da a bane..
Daga jaridar​ Taskar labarai daga hirar idah da NTa Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here