Yan sanda sun haramta al’adar tashe a Kano

0

Yan sanda sun haramta al’adar tashe a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta haramta yin tashe a daukacin jihar Kano baki daya.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Dsp Abdullahi Kiyawa ya ce rundunar ta gargadi iyayen yara da ‘yan mata da samari da su guji saba dokar.

Indai ba’a manta ba tashe al’adar ce da Bahaushe ke gudanarwa daga goman farko na watan azumin Ramadana.

Kiyawa ya ce daukar matakin ya biyo bayan yadda bata gari ke amfani da al’adar wajen yin fadan daba da kwacen waya da ta’amali da miyagun kwayoyi.

See also  RECONSTRUCTION OF THE OWO - IKARE - ARIGIDI - OYIN ROAD IN EKITI STATE!

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci jami’an tsaro su tabbatar jama’a sun bi dokar.

Sannan ya jaddada cewa rundunar ba za ta saurarawa duk wanda ya bijirewa dokar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here