YAN SANDA SUN TARWATSA ZAMAN MAKOKI A JIBIA

0

YAN SANDA SUN TARWATSA ZAMAN MAKOKI A JIBIA
DAga taskar labarai
Yan sanda sunyi yunkurin hana zaman Jana iza ta Alhaji lawali sarkin noma mahaifin Aminu maye.yan Sandan sunyi hakan ne don tabbatar da dokar nan da ta hana taruwar jama a a katsina.
Ganau sunce kwamishinan yan sanda da kanshi yaje har jibia ya kalubalanci yadda aka karya dokar taruwar.
Inda kuma nan take ya kama Aminu maye bisa yadda yana cikin gwamnati yasan da dokar amma yayi mata Karan tsaye.bayan kama Aminu meye,yan sandan sun umurci da kowa ya tashi .
Daga baya, wani yace an sako Aminu mayen kuma masu zaman gaisuwa sun cigaba da zuwa.
A dokar da aka Sanya ma hannu duk Wanda ya Saba ta zai je gidan yari ko tara ko hada masa biyu.
Yanzu an Sanya ido aga cewa ko za a tuhumi aminu maye da wannan karya doka da yayi ko ko dokar ba za za yi aiki akanshi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here