‘Yan Ta’adda Sun Sako Fasinjojin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna Da Aka Sace

0

leadership ta Ruwaito ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun sako 11 daga cikin fasinjojin da suka yi garkuwa da su a hannunsu.

 

‘Yan ta’addan sun kai harin a wani sashe na titin jirginin Yayi da suka Saka bam, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa sana suka Bude wa fasinjoji wuta, inda suka kashe mutane tara tare da yin awon gaba da 62 da suka hada da yara da tsofaffi.

 

Ko da yake an ce an sako wasu mutane biyu da suka hada da Manajan Daraktan Bankin Noma Alwan Hassan, wanda aka ce ya biya kusan Naira miliyan 100 da wata mata mai juna biyu.

See also  ALERU YA KWATO MA MUTANEN YANKARA SHANUN SU.

 

A ranar Asabar, Sheikh Ahmad Gumi ‘Dan Iyan Fika, Malam Tukur Mamu sun ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun sako fasinjoji 11 da aka yi garkuwa da su.

 

A cewarsa, ‘yan ta’addan sun yi niyyar sakin dukkan matan da ke hannunsu amma daga baya sun sako 11 kacal da suka hada da mata 6 da maza 5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here