‘YAN TA’ADDAN DA SUKA ADDABI HANYOYIN JIBIA DA BATSARI… Sunayensu, asalinsu da yawansu

0

Mu’azu Hassan

 

‘Yan ta’adda masu dauke da makamai sun addabi hanyoyin Jibia da Batsari a Jihar Katsina. Suna tare hanya ba dare ba rana. Suna shigowa garin Katsina ta hanyoyin Jibia da kuma Batsari.

 

Jaridun Katsina City News, sun yi binciken gano wace Daba ce ke aikata wannan danyen aikin?

 

Bayan mun kwashe kwanaki muna magana da mutanen kauyukan yankin da jami’an tsaro masu tattara bayanan ayyukan wadannan ‘yan ta’adda a Jihar Katsina, mun gano cewa babban dan ta’addan da ke damun wadannan hanyoyin da shiga Katsina shi ne, Audu Lankai, dan asalin wani kauye ne mai suna Bukur a Karamar Hukumar Jibia.

 

Yana da shekaru kimanin 40 zuwa 45. Yana da yara sama da 200 a Dabarsa. Ana jin yana da bindigu sun kai 50 ko sama da haka.

 

Lankai ya yi sulhu da kauyuka kusan bakwai na kusa da dajin da yake zaune.

 

Ba zai kai masu hari ba, ba zai bari a kai masu su ba. Za su yi noma. Za su yi masa noma. Ba za su hada kai da jami’an tsaro ba. Duk wani shiri na kai masa hari, ko bakuwar fuska, za su ba shi labarin ta.

 

Mun sakaya sunan kauyukan don tsaron lafiyarsa. Lankai shi ne Sarki da Alkali a wannan yankin.

 

Na biyun su shi ne wanda ake kira Bala Wuta. Asalinsa yaron Lankai ne, amma ya yi tawaye ya kafa nasa yaran.

 

Bala yana da shekaru 35 zuwa 40, yana da yara kamar 50, da bindigu sun kai 30, yana iko da yankin Kadoji, Fage da Kwarare.

 

Ya fito daga wata Ruga cikin dajin Kadoji.

 

Na ukun su shi ne Sani Yalo. Ana jin dan asalin garin Yau-Yau ne a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

 

Yaransa 30 ne, yana da bindiga 10. Yalo matashi ne dan shekaru 30 zuwa 35.

See also  YADDA JAMAA ƘOƘARIN SHIGAR DA TSOHIN KUƊIN SU A BATSARI.

 

Duk wani hari da ake kai wa da rana tsaka yaransa ne. Shi ka’idarsa bai yarda da zuwa hari da dare ba. Duk tare hanyar Batsari da Jibia yaran Yalo ne. Mintuna biyar zuwa 10 suke yi su gama su wuce.

 

Yana zaune ne cikin tsaunukan Ruma ta Batsari.

 

Na hudun su shi ne Barumaye. Shi ma matashi ne mai shekaru 30 zuwa 35. Yana da yara 40 zuwa 50 da bindigu kamar 20.

 

Yana yawo tsakanin Gurbi, Tsambe da garinsu Bammi.

 

Yakan ba da hayar yaransa su je su yi ta’addanci su dawo.

 

Wadannan hudun sune Dabar da suka dami hanyoyin Jibia zuwa Katsina, da Katsina zuwa Batsari. Sune kuma ke shigowa har unguwannin da ke gefen Katsina ta bangaren Kananan Hukumomin Jibia da Batsari.

 

Wadannan sune manyan, amma yadda suke samun yaransu kuwa, ‘ya’yan Fulani ne da ke Rugagen cikin daji. Mafi yawansu ba wanda yake kai wa shekaru 20. Yara ne kanana ake ba su bindigu da kwaya.

 

Bincikenmu ya gano duk sato mutum a gida ko daji kudin da za a ba yaro shi ne dubu 10. Sai kuma kudin gadin wanda aka sato har zuwa sakin sa bayan an amso kudin fansa.

 

Wata Dabar Naira dubu daya ce kacal kudin gadi kullum rana, yayin da wata kasa da haka, wata kuma sama da haka.

 

Daga cikin wadanda akan raba kudi da su har da ‘informa’, wanda ya ba da labarin yadda za a dauki wani ko wasu.

 

Sukan dauki hayar wurin da za su ajiye wanda suka dauko da kuma bindigar da za a yi amfani da ita wajen kai hari. Su ma akan cire kudinsu.

 

Katsina City News

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

@ www.taskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here