YANBANGAR SIYASA SUN HANA HORAS DA MA’AIKATAN WUCIN GADI NA HUKUMAR ZABE A KARAMAR HUKUMAR CHARANCHI TA JIHAR KATSINA

0

‘YANBANGAR SIYASA SUN HANA HORAS DA MA’AIKATAN WUCIN GADI NA HUKUMAR ZABE A KARAMAR HUKUMAR CHARANCHI TA JIHAR KATSINA
yau ne wasu ‘YANBANGAR siyasa da Karnukan farauta a karamar Hukumar Charanchi dake jihar Katsina ,suka mamaye harbar model primary ta garin, inda suna waken tawaye da kabilanci Suka Kori malaman zabe, da yanbautar kasa, cewa su ba yan asalin karmar hukumar bane don haka ba su yarda su akin zabe a nan ba. YANBANGAR sun dinga bi aji aji da bulalai suna zagin mutane suna koro su.
Wannan abin kunyar ya faru duk da cewa Akwai jamian tsaro a wurin. Wannan Yasa wasu ke ganin Kamar da sa hannun wasu yansiyasa. Kuma wannan ya dasa ayar tambayya ko jamian tsaro za su iya bada tsaro a zabe mai zuwa
Bayan tata-burza, jami’an INEC a nan Karamar hukumar Charanchi sun kulla yarjejeniya da YANBANGAR siyasa cewa za a bar su shiga horo. Yanzu haka sun rarraba kansu aji aji.
Wannan manuniya ce cewa INEC nada aiki ja a gabanka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here