YARA MILIYAN BIYAR ZAA HAIFA A NIGERIYA

0

‘ YARA MILIYAN BIYAR ZAA HAIFA A NIGERIYA’: inji Masana halayyar dan’adam

Daga Ibrahim Hamisu

Masana ilimin zamantakewar Dan Adam sunyi ittifakin cewa zaa samu yalwar ‘yaya da yawansu ya kai Miliyan biyar a watanni shida zuwa bakwai masu zuwa a Nigeriya, sakamakon wannan zama na Lockdown.

Musa Abdullahi Sufi Wanda masanin halayyar dan Adam ne kuma mai sharhi a alamuran yau da kullum ya bayyana haka a wata da aka yi da shi a cikin shirin Radiyo mai suna Rayuwa da Korona inda ya ce “wannan zaman lockdown wato zaman gida dole yana da abubuwa da dama da yake bijirowa da su, daya daga ciki shi ne yadda ma’aurata suke samun lokaci, a wani lokaci abinda baa shirya masa yakan auku, misali shi ne samun juna biyu wata kila ma a lokacin ba ta gama yaye yaron ba kila yaron ma bai gama samun ingattaciyar lafiya ba, ita ma lafiyarta ba ta gama zama ingantacciya ba.

See also  DAN KAROTA YA SOKAWA WASU DIREBOBI WUKA A KANO

Sufi ya kara da cewa, ”shi ya sa a wannanan lokaci a keso su maaurata su kula da wannan bangare na da samar da tazarar haihuwa, domin samun ingantacciyar lafiyar uwa da jiririnta, da kuma gida gaba daya, domin uwa mai ingattaciyar lafiya ita ce ke samun lokacin da ta ke kula da gidan da mai gidan da ‘yayan ta da tsabtace gidan da muhallinta, musamman a irin wannan lokaci,

Da haka ne mace za ta samu karfin kula da tarbiyya da tsafta kamar yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here