Yunƙurin Kutsawa A Baddala Alƙaluman Bayanan INEC Bai Yi Nasara Ba, Inji Farfesa Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa sababbin dabarun killace alƙaluman zaɓe ta hanyar na’urori da manhaja sun tabbatar da cewa zamanin baddala sakamakon zaɓe ko yin kutse cikin rumbun tattara bayanai ya wuce.

 

Yakubu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da ƙungiyar YIAGA Africa ta shirya a Abuja.

 

Ya ce ko a zaɓen gwamna na jihohin Ekiti da Osun da aka yi a baya-bayan nan, ‘yan kutse daga ƙasashe daban-daban, har da wasu daga nahiyar Asiya, sun yi ƙoƙarin kutsawa rumbun tattara bayanai na INEC ta cikin manhaja domin su baddala alƙaluman zaɓen, amma ba su yi nasara ba.

 

Ya ƙara jan kunnen ma’aikatan hukumar da masu sa-ido cewa tilas sai an ƙara sa ido sosai kuma an ƙara ƙarfafa hanyoyin hana ‘yan kutse shiga manhaja domin baddala sakamakon zaɓe.

 

Ya ce: “Kuma mun ƙara jaddadawa da ƙara ɗora nauyin kulawa ga injiniyoyin mu cewa kada su yi sanyin jiki wajen hana duk wata ƙofar da ‘yan kutse za su iya kai farmaki a manhajar tattara sakamakon zaɓe.

See also  Buhari ya jajanta wa iyalan sojojin da aka kashe a Neja

 

“Waɗannan hanyoyi biyu da mu ka shigo da su yanzu su na da ingancin da babu yadda masu baddala sakamakon zaɓe ko masu kutse za su iya yin nasarar shiga rumbun tattara bayanai ko manhajar alƙaluman zaɓe.

 

“Hanyoyin biyu, wato tsarin amfani da na’urar BVAS da kuma manhajar IReV, su na da ingancin killace dukkan bayanai da alƙaluman zaɓe ba tare da shakkun an kutsa an baddala su ba.

 

“Ita na’urar BVAS aikin ta shi ne tura hoton tambarin yatsan mai dangwala ƙuri’a da kuma tantance fuskar wanda ya dangwala yatsa bisa na’urar, sannan kuma ta kwafi fom na sakamakon zaɓe (EC8A) ta tura cikin manhajar IReV.”

 

A nasa jawabin, Babban Daraktan YIAGA Africa, Mista Samson Itodo, ya yi kira ga INEC da ta ƙara wayar wa da jami’an ta da waɗanda za a ɗauka aikin zaɓe nan gaba kai sosai domin su ƙara fahimta tare da samun ƙwarewa a dukkan hanyoyin da za a bi domin tattarawa, turawa da killace sakamakon zaɓe sun gudana a sauƙaƙe.

Majiya: RARIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here