YUNWA DA BAKIN TALAUCI YANA NAN TAFE

0

YUNWA DA BAKIN TALAUCI YANA NAN TAFE
Binciken hadin gwaiwa @Taskar Labarai

An gudanar da wani bincike na hadin gwaiwa tsakanin wata kungiya mai suna Green Light Project, da jaridun Taskar Labarai da The Links na halin kunci, talauci da rashin abinci wanda jihar Katsina zata shiga nan gaba kadan.

Binciken mu ya tabbatar cewa duk abincin da ake da shi a shaguna da dakuna ajiya basa iya wuce sati biyu nan gaba zasu kare karkaf.

Kuma yadda kamfanoni ke aiki rabi da rabi ba zasu iya cike gibin da ake bari ba, wani mai babban shago a jihar Katsina ya bada yadda suke sayen kaya su zuba a shagunan su ada. Yace muna zuwa kasuwa sau biyu a sati sannan kamfanoni na kawo mana har inda muke, duk da haka kafin zuwa kasuwar sai kaga komai ya kare, yace yanzu ba zuwa kasuwar kuma kamfanoni basa kawowa don haka, abin da muke da shi muke saidawa duk wanda ya kare ya kare kenan.

A binciken mun bi duk shagunan da aka amince su sayar da kayan su mun iske duk kantocinsu sun yi kasa, kuma wasu abin da ya kare ba ranar da za a sawo wani.

Mun bi shagunan dake cikin lunguna munga yadda ake sayan kayan da suke da shi amma shima da ya kare sai dai a jira.

Wani mai babban shago ya tabbatar mana cewa, a shagon shi, abubuwa da ya wa sun kare sai kuma waya yake a Kano inda ake kawo masu suna kaffa-kaffa na su saki kayan baki daya, yace yana da wata taliya sama da katan dubu uku amma duk an kame ta, an biya ajiya kawai yake.

Binciken mu ya gano a kwai kayan abinci a shagunan kasuwa da aka kuble da wasu ma’ajiya, amma ko su duk ranar da aka bude kasuwar sau daya sau biyu sau uku sun kare gashi lamarin ba ranar karewa.

Binciken ya gano Kano in da aka dogara da ita suna taka tsantsan su saki abin da suke da shi baki daya a saye.

See also  MATA ADON GARI NI'IMAR DUNIYA

Binciken ya gano, kamfanoni na aiki rabi da rabi ne, abinda suke samarwa kamar kashi hamsin ne na abin da suke kaiwa kasuwa a da don haka, wanda za su rika kawowa ba isa zai yi ba.

Mun yi magana da wani manajan gudanarwar kamfanin abinci dake Legas, yace abin da suke yi sai sun yi tsaye suke kawo shi a Arewa don mabukata a Legas ke amshewa, yace kuma gwamnatocin kudu na uzura masu akan su rika ba jama’ar abin da suka saraffa don haka kingi ke zuwa arewa. Su kuma su ciccira.

Binciken ya gano abincin da aka noma wanda ke karkara shi ne za a koma mawa, wanda binciken mu ya kasa gano ko zai iya rike mu zuwa wani tsawon lokaci?

Binciken mu ya gano yanzu ‘yan kasuwa basu kara kudi ba, ga kayan masarufi amma tabbas in na hannu ya kare suka koma kasuwa kudin sai in da lamba ta nuna.

Binciken ya gano ana shirin shiga wani yanayi na kana da kudin baka iya samun abin da kake so sai dai abin da ya samu kuma ka gani ka saya.

Binciken mu ya gano gwamnatin bata shirin komai ko dai na wayar da kan jama’a ko tanadi ko shirin ko ta kwana akan wannan hali da ake neman shiga.

Binciken yayi kira ga gwamnati su fara shirin tarbar halin da za a shiga da kuma shirin Coronavirus lokaci guda, don in ba ayi taka tsantsan ba ana iya maimai ta abin dake faruwa a Kano, in da mutane ke mutuwa a gidajen su amma ba a san dalilai ba.
________________________________________________
Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta dake a www.taskarlabarai.com da kuma ta Turancinta The Links News a www.thelinksnews.com. Green Light Project kungiya ce mai nazarin halin da ake ciki mai ofis a Legas duk ra’ayi ko sako aiko ga kira ko WhatsApp 07043777779 da 08088895277

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here