ZA A KAI WANI SANATAN JIHAR KATSINA KOTU

0

ZA A KAI WANI SANATAN JIHAR KATSINA KOTU

@Jaridar Taskar Labarai

Yanzu haka wani kamfani da ke sarrafawa da siyar da kwanon alminiyum, ya shirya tsaf don maka wani Sanata daga Jihar Katsina a gaban kotu.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa, kamfanin zai shigar da Sanatan kara ne a kotuna guda biyu; daya ta Shari’ar Musulunci ce, a kan zargin saba alkawari da cin amana, wanda ana iya yi wa Sanatan bulala idan an same shi da laifi.

Dayar shari’ar kuma za a shigar da ita a kotun Majistre ce don tilasta wa Sanatan biyan kudin da kamfanin ke bin sa bashi cikin gaggawa da kuma yi masa hukunci a kan saba alkawari.

Shi dai wannan Sanatan ya karbi bashin wannan kamfanin ne tun kafin ya zama lashe zabe na kayan gini har na sama da Naira miliyan 30, ya yi kwangila, an kuma biya shi kudinsa, amma ya ki biyan kamfanin kudin kayan da ya karba.

Don haka kamfanin da ya ga Sanatan ya zama kato sai Allah ya isa, yake da niyyar shigar da kara kotu don a kwato masa hakkinsa.

Wannan Sanata mutanensa na tsananin kuka da shi, ba ya iya samar masu aiki, taimako, ko tallafin rage radadin rayuwa, kamar yadda sauran ‘yan’uwansa kan yi wa mutanen yankinsu.

See also  Yajin aikin Malaman Jami’o’i baraza ne ga ilimi a Arewacin Kasar nan

Kwanan nan ya samu gurbin daukar ma’aikata guda biyu a Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (Federal Inland Revenue), gurbi daya sai ya ba wata yarinya tsaleliya wadda suke mutunci ‘yar Jihar Imo. Gurbin guda kuma ya ba wata yarinya kyakykyawa daga Karamar Hukumar Jibia. Ita ma yarinyar an ce suna mutunci gaya.

Mutanensa na zargin in an ba shi aikin da ya shafi inganta mazaba, maimakon ya kira ‘yan kwangila na cikin yankin ya ba su kowa ya amfana, sai ya siyar da aikin ga Yarbawa ko Inyamurai, wadanda in sun tashi zuwa don su yi aikin, hatta abincin da za su ci da abinsu suke zuwa, wanda in ‘yan gida ya ba wadanda za su amfana suna da yawa.
____________________________________________
Taskar Labarai jarida ce a bisa yanar gizo da ke a www.taskarlabarai.com tana da yan uwa guda biyu Katsina City News da ke a www.katsinacitynews.com da kuma The Links News da ke www.thelinksnews.com. da kuma bisa sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here