ZA A KAMMALA MATATAR MAI TA GARIN MASHI A SHEKARAR 2021
A ranar Talatar nan ne, Kamfanin Agency Reporter ya haƙalto, Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Jamhuriyar Niger, Mahammadou Issoufou suka shaida ƴarjejeniyar gina matatar man, wadda ƙaramin Ministan albarkatun man fetur Ibe Kachikwu da takwaransa Minisitan Makamashi Foumakaye Gado suka sanya wa hannu, inda ƙaramin Ministan albarkatun Man ya bayyana cewa an cimma matsayar za a kammala aikin gina matatar man ta garin Mashi da ke a jahar Katsina a shekarar 2021.
Mr Kachikwu ya bayyana haka ne a taron manema labarai a Abuja, inda ya ƙara da cewa indan an kammala matatar za ta iya samar da ganga 150,000 a rana.
Ministocin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimmwa kan gina matatar man a tsakanin Nigeriya da Niger a ranar Talatar a fadar gwamnatin Nigeriya da ke Abuja.
Bayan dogon nazari da bincike da aka aiwatar kan yadda za a gudanar da aikin na gina matatar man, wanda hakan ya janyo ɗibar wa’adin shekaru uku dan gudanar ingantaccen aikin.
Ministan ya ƙara da cewa wannan wata dama ce ta ƙara faɗaɗa ayyukan matatar man fetur ta Kaduna, duk da cewa a jahar Katsina ake gina matatar amma za ta ƙara faɗaɗa ta jahar Kaduna ta hanyar janyo fayif na mai daga jamhuriyar Niger har zuwa Kaduna.
Kwamitin kula da Kammafanin mai na ƙasa NNPC sun ce duk da dai dararjar man jamhuriyyar Niger bai kai dararjar na ƙasar Nijeriya ba, amma su na da makusanciyar daraja da ta kai kaso 90 % 100 bambancin da ke akwai na kaso 10 ba wani abu bane.
Da ya ke magantawa kan batun gina matatar, Ibrahin Zakari wanda yana ɗaya daga cikin masu zuba hannu jari a Nigeriya, ya ce aikin gina matatar zai laƙume dallar Amurka biliyan biyu.
Ya yi kuma fatan za a bai wa Kamfanin na Blak Oil Energy ƙaso mai tsoka dan suma aikin gina matatar.
Ya ƙara da cewa yana fatan dai, Shuwagabanin ƙasar guda biyu sun riga sun kammala komai na aiki.
Da ya ke magana game da masu zuba hannu jari, ya yi fatan a samu wani wanda zai zuba dalla biliyan biyun a aikin.
Wanda zai fito daga asusun ƙasashen ketare irin su US da Canada da India da kuma Gabas ta tatsakiya.
Ya ce ƙasar nan za ta samar da ganga 50,000 yayin da jamhuriyar Niger za ta rinƙa samar da ganga 100,000 .
Zakari ya ƙara da cewa wannan aiki na iya ɗaukar su tsawon shekaru biyar kafin a kammala shi kwata kwata, sai dai kuma idan an kammala aikin zai samar da gurabun aiki sama 2500 ga ƴan Najeriya.