ZA A KASHE ABACHA DA ABIOLA?
Na Dade ina labarai wadanda suke hannunka mai sanda da kuma hasashe.kuma abin da na rubuta ya tabbata gaskiya.
A shekarar 1994 na rubuta wani labari ya fito a fuskar farko na jaridar Al mizan.duk abin da na fada sai da suka faru.
Na rubuta cewa za a kashe Abaca da Abiola, lokacin Abaca yana shugaban kasa Abiola kuma yana shugaban yan adawa, yaci zabe an hana shi.Abaca yana bisa mulki, Abiola yana tsare a hannun gwamnati.
A 1994 na rubuta labari na a 1998 da Abiola da Abaca duk suka mutu a hanyar da ake jin cewa an kashe su ne ta yadda za a dauka mutuwar Allah ce.
Abaca ana zargin yaci wani tuffa , tare da wasu matan India.Abiola ana zargin shayi da ya kurba. Allah shine masani.Kalli shafin jaridar ta Al mizan din da ta fito a wancan lokacin…Danjuma katsina