Za’a dauki Babban matakin hukunta masu safarar yara a duniya

0

Za’a dauki Babban matakin hukunta masu safarar yara a duniya

Inji MDD

Daga Zubairu Muhammad

Sakataren majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana haka a taron ranar yaki da safaran Mutane na Duniya.da ya gudana a makon jiya.
Da yake jawabi a wajen taron Babban Sakataren Mr. Antonio Guterres yace; safaran Mutane babban laifi ne a Duniya, ya na kawo rashin aminci, rashin daidaiton al’amura, da kuma rikici a duniya. Safaran Mutane yana zuwa ne daga mutane mara sa ki shi, wadanda basa fatan alkairi a rayuwar su, sun kware wajen tauyema mutane ‘yancin su.

Sun mayar da Yara da matasa kamar ‘yan gudun Hijira, amma sun fi matsama Mata da ‘yan Mata wajen wannan muguwar sana’ar, musamman da yake mata ne ake tilasta masu yin harkar karuwanci, ko a matsa musu yin auren dole, ko kuma a bautar da su ta hanyar da batadace ba.
Muna sane da yadda aka mai da safarar mutane kasuwanci a kasashe daban daban na Duniya.
Safaran mutane yana daukar sabon Salo a boda_boda ma’ana kan iyakokin Qasashe , da muke da su na Duniya. Xan haka Qasashen Duniya ya kamata su hada kansu su ce sun gaji da wannan muguwar al’adan ta Safara, hakan ne kawai zai kawo canji a Duniya.

See also  Zanga-zanga Ta Ɓarke A Amurka Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa

Majalisar Dinkin Duniya tana nan tana tsara wasu sababbin dabarun daukar matakin hukunta masu Safaran Mutane da kuma kare wadanda ake musu Safaran, mu kuma nuna musu goyon baya. Dole mu fi ba wadanda abun ya rutsa da su fifiko, kuma za mu kara daukar tsauraren matakai na dakile safaran Mutane, Fasakauri, sabuwar hanya ta bautar da Mutane, da kuma sa ido akan mai ke shiga kasashen Duniya.

Tsare_tsare sun yi nisa a Duniya wajen rage yawan Mutanen da suke gudu zuwa wata qasa saboda samun rayuwa mai kyau, muna sa rai a watan Disamban nan komai zai kammala. Ya zama ko wata Qasa tana kokarin warware fitintinu da suke fama da shi, kuma su yi kokari wajen kawar da Safaran Mutane gaba daya a Qasashen su.
Saboda haka a wannan rana ta yaki da Safaran mutane, muna kira da babban murya akan kasashe su hada Hannu wajen yakar wannan al’amari, kuma su inganta rayuwar Mutanen Kasar su, ta haka ne kawai za’aiya kawar da wannan al’amarin gaba daya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here