Zaa sanya Kyamaririn sa’ido a Titunan Jihar Kano

0

Zaa sanya Kyamaririn sa’ido a Titunan Jihar Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje , ya kammala aikin sanya kyamarorin sa ido a wasu manyan titunan Kano domin ingantawa da saukaka Ayyukan tsaro a jahar Kano.

Salihu Tanko Yakasai, Mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai Salihu Tanko yakasai ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya nuna bidiyon jami’an‘yan sanda da ke kallon motsin mutane da ababen hawa a kan manyan titunan jahar kano

Duk da cewa Kano ta kasance daya daga cikin jihohin da suke da zaman lafiya a Najeriya tun shekaru biyar da suka gabata, amma mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai daina kokarin karfafa tsaro a jihar ta Kano ba

See also  Minister Tours Terminal 2 of MMIA, Calls It Testament To Infrastructure Development 

Domin kuwa gwamnatinsa ta sanya kyamarorin sa ido a kan manyan hanyoyi.

Ana sarrafa na’urorin (CCTV) ne daga wani daki na musamman a hedikwatar ‘yan sanda, na jihar Kano. “in ji Salihu Tanko Yakasai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here