Zaben Ekiti: zababben gwamna, Oyebanji, ya musanta zargin sayen kuri’u.

0

Zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya ce shi ko jam’iyyarsa ta APC, ba shi da hannu a cikin sayen kuri’u da ake zargin an tafka a zaben ranar Asabar da ta gabata, wanda ya lashe zaben.

Oyebanji ya bayyana haka ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar litinin.

Ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdulahi Adamu; Gwamna Kayode Fayemi (Ekiti), Abubakar Badaru (Jigawa) da Atiku Bagudu (Kebbi) da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari na yanzu, Otunba Niyi Adebayo.

Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan an gabatar da shi ga shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, Oyebanji ya ce bai yadda a sayi kuri’u ba a rumfar zabe da ya kada kuri’ar sa.

See also  Zaɓen Edo: Gwamna Wike ya yabi INEC da jami'an tsaro

Zababben gwamnan ya ce ya lashe zaben ne bisa yadda gwamnatin jihar mai barin gado karkashin jagorancin Gwamna Fayemi ta yi, inda ya taka rawar gani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here