ZABEN FIDDA GWANI NA APC: Me Ya Faru A Zaman Sulhun Da Aka Yi? 

0

Mu’azu Hassan

A jiya Talata 21/05/2022 an yi wani zaman dinke barakar da ta bullo a jam’iyyar APC bayan zaben fid da gwani na Gwamna a gidan gwamnatin Katsina.

Zaman, wanda ya wakana tsakanin wadanda suka yi takarar neman APC ta tsayar da su da kuma shugabannin jam’iyyar da Gwamnan Katsina.

A bangaren wadanda suka yi takara da suka halarta sune; Dattijo Mataimakin Gwamnan Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, sai wanda APC ta tsayar don yi mata takara, Alhaji Dikko Radda, sai Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Alhaji Farouk Jobe, sai tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Dakta Mustafa Inuwa. Sai Alhaji Abdulkarim Dauda Daura.

Wadanda ba su samu damar halarta ba sune; Alhaji Abubakar Saddiq ‘Yar’adua. Ba ya kasar, amma ya aiko da uzurinsa. Alhaji Abbas Masanawa, shi ma ya aiko da uzurinsa. Sai Ahmad Dangiwa.

A zaman ba a sanya Alhaji Umar Tata a cikin lissafi ba, domin ya shelanta ficewa daga APC zuwa PDP.

A bangaren jam’iyyar APC, sun samu wakilcin Shugaban jam’iyyar da Sakataren jam’iyyar da Mataimakin Shugaba na Jiha, Alhaji Bala Abu Musawa da Sakataren Tsare-Tsare na jam’iyyar.

Majiyoyi daban-daban sun ba mu bayanin yadda taron ya gudana.

Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya fara magana, wanda ya ba da hakuri da kuma neman a kai zuciya nesa da hada kai don a yi nasarar zaben 2023.

Wanda ya fara magana bayan Gwamnan Katsina shi ne, Dattijo Alhaji Mannir Yakubu, wanda ya ce sun sallama komai, sun bar wa Allah, kuma shi da magoya bayansa za su yi aiki tsakani da Allah don nasarar APC a zaben 2023.

Alhaji Mannir Yakubu, ya yi magana mai cike da hikima da sallamawa.

Daga nan sai aka zo wajen Alhaji Farouk Jobe, wanda ya ce an yi zabe, Allah ya ba daya daga cikin su. Don haka za su yi komai don mara masa baya.

Jobe, ya jawo hankalin a kan hatsari da halin da kowa ka iya shiga in har aka fadi zaben saboda rarraraba.

See also  2023: "Kiristocin arewa ba za su zabi musulmi da musulmi ba" - Shagari

Ya kuma yi gargadin hatsarin abin da za su fada in ya zama ya yi daban aikin su.

Da aka zo kan Alhaji Abdulkarim Dauda cewa ya yi, maganar a ba da hakuri ma ba ta taso ba. An shiga zabe, dole dama daya ne zai yi nasara. “Kuma Allah ya ba mutum daya, sai mu yi aikin da Allah zai kai mu ga nasara,” in ji shi.

Da aka zo kan Dikko Radda, wanda jam’iyyar APC ta tsayar ya yi mata takara kuwa, ya nemi goyon bayan kowa ne. Ya kuma ce ya bi duk ‘yan takarkarin da suka fafata.

Ya ce ko a wannan satin ya je gidan Abbas Masanawa shi da Ahmad Dangiwa, kuma sun tattauna yadda za a ci nasara.

Da aka zo kan Dakta Mustafa Inuwa, tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina kuwa, kin magana ya yi. Ya ce shi ba zai ce komai ba. Duk abin da zai ce ya ce a taron manema labarai da ya kira kwanaki kadan bayan zaben.

Dattijo Mannir Yakubu ya jawo hankalinsa da cewa, dukkanin su sun yi magana, kuma an yada ta. Ya ce nan taro ake yi. Ya kamata yadda kowa ya yi magana, shi ma ya yi.

Amma dai duk da haka, Mustapha Inuwa ya ki magana. Ya tsaya a kan matsayarsa ta farko ta cewa ya riga ya yi magana, ba zai kara wata ba.

A bangaren shugabannin jam’iyya, su ma sun yi magana. Duk majiyarmu sunce kowa an fahimce shi, amma sakataren jam iyya ne kawai aka kasa fahimtar sakon sa a maganar da yayi. inji masu bamu labari.kafin a tashi gwamnan katsina har kwangilar kawo mota ya ba kamfanin sakataren jam iyya.motar da za a ba .shugabar mata ta jam iyyar APC.

haka aka tashi taron. Ana sa ran za a sake wani taron gaba kadan .

Katsina City News

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

@ www.taskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here