Zaben Musawa/Matazu: Wa Ya Gayyyato ’Yan Daba Har Aka Yi Kisan Kai?
…..Aka jikkata wasu masu yawa
@ Binciken Katsina City News da hadin gwiwar CAEV Nigeria
Bincikenmu ya tabbatar mana a duk fadin Jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya, a Jihar Katsina ne kadai aka kashe mutum a zaben fid da dan takarar Majalisar tarayya na APC wanda ya gabata a garin Musawa ta jahar katsina a ranar jumma a 27/5/2022
A kan haka jaridun Katsina City News da wata Kungiyar kasa da kasa masu yaki da amfani da ’yan daba a wajen zabe (Campaign Against Election Violence) mai samun goyon bayan USAID, suka gudanar da binciken gano wa ya gayyato ’yan bangar da suka kashe mutum suka jikkata wadansu a zaben da ya gudana ranar 27/5/2022 a Musawa.
Binciken mu ya gano an kashe wani matashi daya mai suna Abdul Musa, dan asalin Karamar Hukumar Matazu, amma mazaunin Kano, an kuma jikkata mutane 20, wasu na jinya a gidajensu, ya zuwa lokacin rubuta rahoton shida daga cikinsu suna kwance a Asibitin Kwararru da ake kira FMC ta Katsina.
Binciken mu ya tabbatar mana wasu motocin da aka dauko ’yan dabar da su suna a wajen ’yan sanda, kuma sun kama wadansu daga cikin ’yan dabar da kuma makaman da suka shigo da su.
Binciken mu ya gano duk motocin da aka Barnata na daya daga cikin yan takarar ne mai suna Ali abdu.wanda aka fi sani da janaral
Binciken mu ya tabbatar Da safiyar da za ayi zaben an ga wadannan gungun yan Daba a cikin dajin tsakanin musawa da matazu sun shirye shiryen zuwa wajen zaben.
Mun ji zarge zarge na wasu gidajen da aka ajiye wadannan yan daba suka kwana daga alhamis 26/5/2022 zuwa jumma a 27/5/2022.
Mun yi magana da ’yan takara uku cikin hudu da suka yi takara; Ali Maikano da Ibrahim D. Murtala, Ali abdu Wanda aka fi sani da janar kowannen su ya fada mana abin da ya sani.ba mu samu magana daya daga yan takarar da ake ma labari da Mai Zamani ba, amma mun samu wata takarda da ya rubuta ta korafi a kan zuwan ’yan daban.
Takardar da aka tabbatar mana ya baiwa gwamnan katsina kwafi da kuma kwamitin korafin zabe da uwar jam iyyar APC ta kafa,
Mun samu tabbacin Wanda ya zarga a takardar Alhaji Bala Abu musawa ya umurci lauyoyin shi sa su shigar da kara a kotu kan bata masa suna da yayi a rubutun.
Binciken mu ya tabbatar mana duk ’yan dabar da suka shigo garin a ranar zaben ba ’yan garin Musawa ko Matazu ba ne. Baki ne da aka dauko daga jihohi makwabta. Musamman jahar Kano,
Kowane bangare na zargin dayan a kan sune suka kawo ’yan dabar daga makwabtan Jihohin Katsina, kamar yadda muka gani, bisa bayanan da muka samu na wadanda muka yi magana da su, ’yan takara uku da takardar korafi da dan takara na hudu ya rubuta.
Binciken mu na jin ta bakin mutanen garin Musawa da muka magana dasu.Ra ayinsu yafi zargin wani Dan takara mazaunin Kano wanda ya fito daga cikin yan takarkarin da suka fito daga karamar hukumar Matazu. Wanda ya taba rike kujerar shekarun baya da suka wuce Wanda ake Kira da Ibrahim D Murtala
Kakakin rundunar ’yan sanda na Jiha Katsina, SP Gambo Isah ya shaida wa kwamitin binciken name cewa, rundunar ’yan sanda tana zargin wani dan takara cikin ’yan takarkarin da dauko ’yan daba daga Kano. “Yanzu haka muna neman sa don ya zo ya ba da nasa bahasinsa,” , in ji shi.
SP Gambo Isah ya ce sai sun same shi, sun kuma kammala bincikensu, Hukumar ’yan sanda za ta iya fitar da matsayar ta a kan rikicin da aka yi a zaben Musawa na Dan Majalisar Tarayya.a ranar 27/5/2022.
Binciken mu ba akan anyi zaben ko a a, bane .amma bincike ne akan Amfani da yan daba a filin zabe.
Binciken na Katsina City News da CAEV Nigeria yana ci gaba. Har yanzu muna magana da wadanda abun ya shafa da ganau a Musawa inda aka yi rikicin.
Cikakken rahoton na hadin gwiwar Katsina City News da Kungiyar Campaign Against Election Violence mai samun goyon bayan USAID zai fito gaba kadan.
Zai zo da bayanan da kowa ya bayar da matsayar Rundunar yan sanda ta jihar katsina.
An tsakuro bayanin ne daga Rahoton da ake tattarawa akan rikicin.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
0704377779.08137777245