ZUWA GA DANMAJALISSAR JIHA NA KARAMAR HUKUMAR RIMI

0

ZUWA GA DANMAJALISSAR JIHA NA KARAMAR HUKUMAR RIMI~~~ An dade ana ruwa

Ranaka ya dade barka da wannan lokaci, ya hakuri da jama’a? Fatan dai kana cikin koshin lafiya.

Na rubuto ma wannan wasikar ne domin yi maka tuni kan nauyin da ke rataye a wuyanka na al’ummar da kake wakilta, duba da cewa ba su da wani wakili da ya fi ka a wajensu, domin kuri’arsu suka sanya suka zabe ka.

Ranka ya dade gaskiyar magana ya kamata ka farka daga wannan nannauyen baccin da kake, e mana nananuyan bacci, domin akwai alkawurra da yawa a kanka da ka daukar wa mutane, kuma ya kamata a ce ka cika masu.

Zan fara yi ma tuni ne da Mazabar da na fito wato Fardami, ranka ya dade a wasu darare cikin shekarar 2019 ka yi wa mutanen wannan yanki alkawarin hanya, ko da yake ko a lokacin na san ba gaskiya ka fada ba, domin baka iya yin hanyar kuma baka iya sawa a yi ta, suma rashin sani ne kawai ya sa suka laminta da kai, in tuna ma hanyar ne? To ita ce hanyar da ta tashi daga Rimi ta zarce har bakin gadar Kanyar uban daba.

Mu aje wannan mutane kauyen Bidi/ Yakasai a ranar ka yi masu alkawarin yi masu magudanan ruwa in zaka tuna, to gaskiya ko ba kome ya kamata ka cika masu wannan alkawari, saboda dai wadanan magudanan ruwa basu da wani yawan da ko cikin kudin ka ba zaka iya yinsu ba, musammana duba da cewa alkawari ka yi.

Haka abun yake a ‘Yarmudi nan ma kasan akwai farfagandar da ka shirya masu, ina rokonka don Allah ka daure ko farfagandar ce ka kara shirya masu.

Na taba jin yaranka da kai kanka a shekarar 2019 kana farfagandar kai korafin yin hanyoyin cikin garin Rimi da samar da ruwan sha a cikin garin Rimin da kuma kai korafin gyara asibitin Rimin. Ranka ya dade ina wadanann zantuka suka kwana? Koko an ci muriyar ganga?

Ranka ya dade na ji Mutanen iyatawa na kuka da cewa akwai wani dan karamin alkawari tsakanin ka da su na saya masu wasu kwamfutoci a makarantar sakandire din su. Haba ranka ya dade wannan fa ba wasu kudade bane da za a kashe masu yawa, ko dan alawus da kake samu na matsayin shugaba a majalissa ai ka cika masu wannan alkawari.

See also  JOBE YA ZAMA NA FARKO A BIYAN KUDIN FOM. na takarar gwamna.

Mutanen Makurda kullum cikin kuka da kai suke ranka ya dade, sunce ka ce masu wannan karon gwamnatinsu ce, za a diba bukataunsau a yi kokarin ganin an magance, amma sun jika shiru.

Ranka ya dade hanyar na da kayi farfaganda da ita a lokacin zabe, wato hanyar Maje zuwa Karare ina aka kwana ne? Ko dama ta baya ta raggo aka yi masu. Ya kamata a yunkura don ganin wannan hanyar ta kai bantenta.

Na ji dadi sosai da naji ance ka yi tsaye wani matashi ya samu aiki kwanaki, lallai dole mu yaba maka a nan.

Sai dai abin da na kasa ganewa shin zagaye makarantar da kayi a Abukur da gyara famfo shi ne aikin da zamu yi tutiya da shi mu ce ka yi a karamar hukumar Rimi? Ko kuwa wannan cikin kudin aljihunka kayi su?

Ranka ya dade muna ta ganin abokan aikin ka suna raba kayan tallafawa al’umma kai har da ma wanda bana yazo majalissar wato mai wakiltar Malumfashi. Shin mu a nan Rimi haka zamu kare? Ba sidi ba sadada?

Ko dan Form din Jamb ya gagara kuma na ga wadanda suke tare da kai suma kamar fankam fayam suke, saboda kwanaki na san wani yaron ka na neman wata kujera ta Unit Head a bangaren lafiya, amma ka gaza yin magana ya samu wannan kujera duk da ya cancanta, haba ranka ya dade, tunda hanyar garinsu ta gagara ida wa ai da ka taimaka ka sa mashi hannu duba da yadda yake yinka ba dare ba rana?

Ina fatan zan samu amsoshin tambayoyi na domin fitar da ni daga halin da nake ciki kafin rubutu na na gaba. Ina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here