ZUWAGA JARUMI NUHU ABDULLAHI (MAHMUD A CIKIN SHIRIN LABARINA)
Daga Ishaka Usman Wali
Nayi matuƙar mamaki irin yadda na kalli hirarka da BBC HAUSA a shirinsu na DAGA BAKIN MAI ITA inda sukaso suji tarihinka
Kaikuma saika nuna musu cewa an haifeka a garin kano kayi primary da secondary duk a jihar kano. Hakika naji babu dadi sakamakon irin yadda naga LA juyawa ƙauyenku baya saboda yanzu rayuwarka taci gaba kuma nayi mamaki matuka.
Inaso wadanda suka kalli shirin Susan cewa an haifi NUHU ABDULLAHI awani kauye da ake kira tudun bichi akaramar hukumar danko wasagu jihar kebbi, nuhu yayi model primary school a tudun bichi inda ya zarce izuwa garin wasagu domin shiga makarantar secondary school maisuna GOVERNMENT ARABIC AND ISLAMIC SECONDARY WASAGU a lokacin marigayi malam jafaru yana principal inda malam abubakar na diri yake mataimaki.
Nuhu abdullahi shine house captain a wasagu house inda shikuma abokinsa maisuna habibu random yake house captain a sakaba house. Nasanshi yasanni domin kaninsa Aliyu Abdullahi abokinane kuma munyi kwana daki daya dashi nuhu abdullahi.
Lokacinda ina sabon shiga makarantar akwai wani prefect maisuna Tijjani A Garba kanin matar yayana ne shine wanda ya daukeni yakaini prefect room na ringa kwana acan dukda ba house dina bane domin ni ina danko house ne wanda Nura yake jagoranta.
Nuhu Abdullahi yasha aikina na debo masa ruwa a bokiti idan zaiyi wanka dasauran dawainiya dayake sakani sakamakon nine yaro kuma junior a dakin dalilin dayasa bansha wata wahalaba kenan saboda mun shaku daduk wani prefect a makarantar.
Bayan anyi shirin gina masallacine Nuhu yadan sami sabanin fahimta da Malam abubakar na diri vice principal wanda shine yayi sanadiyar barinsa makarantar a lokacinda yake gab da rubuta junior waec inda yakoma lagos dazama gurin yayansa maisuna Abdulrahman wanda shine yayi sanadiyar shigarsa sanaar film acan ne yaci gabada karatu har Allah ya taimakeshi ya kammala jamia.
Duk rintsi da irin niimar dakake ciki bai kamata kacire sunan mahaifarka ashafin tarihin rayuwarkaba domin koba komai wadannan yan uwan naka sune sukeyi maka adduar da fatar alkhairi kuma sune suke alfaharin cewa dan uwansu yasamu daukaka.
Dafatar Allah yabaka ikon sanin haƙƙin mahaifarka, Amin